1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasar Nijar

July 4, 2010

A ranar 3 ga watan Janairun 2011 ne 'yan Nijar za su zaɓi sabon shugaban ƙasa

https://p.dw.com/p/OAUl
Hoto: AP

Hukumar zaɓen jamhuriyyar Nijar ta sanar da cewar, a cikin watan Janairun shekara mai zuwa ne - idan Allah ya kaimu al'ummomin jamhuriyyar Nijar za su jefa runfunan kaɗa ƙuri'a domin zaɓen mutumin da zai shugabanci ƙasar - a karon farko tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Tandja Mamadou. A ranar ukku ga watan na Janairu ne ƙasar za ta yi zaɓukan 'yan majalisar dokoki da kuma na shugaban ƙasa domin sake mayar da ƙasar bisa turbar dimoƙraɗiyya, inda kuma za'a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar a ranar 14 ga watan na Janairu - idan har buƙatar hakan ta taso - kamar dai yadda hukumar zaɓen ƙasar ta Nijar ta bayyana.

A halin da ake ciki kuma taron shugabannin ƙungiyar kasuwar tarayyar yammacin Afirka ECOWAS daya gudana a ƙasar Cape Verde ya bayyana gamsuwar sa game da shirye shiryen da hukumomin mulkin sojin Nijar ke yi na komawar ƙasar bisa tsarin dimoƙraɗiyya kasancewar itama mamba ce a ƙungiyar gabannin dakatar da ita saboda juyin mulkin. Dakta Aliyu Idi Hong, ministan ƙasa a ma'aikatar kula da harkokin wajen Nijeriya, kana shugaban taron ministocin ƙetare na ƙungiyar dukkan shugabannin ECOWAS sun yi na'am da huɓɓasar da hukumomin mulkin sojin ke yi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu