1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban kasa a Bangladesh

Abdullahi Tanko BalaDecember 28, 2008

Ƙasar Bangladesh za ta koma tafarkin Dimokradiyya bayan shekaru biyu na mulkin soji.

https://p.dw.com/p/GOK6
Yan takarar neman shugabancin ƙasar Bangladesh Sheikh Hasina ta jamíyar Awami League da kuma Khaleda Zia ta jamíyar BNP.Hoto: AP/DW

Bayan tsawon shekaru biyu a ƙarkashin kulawar gwamnatin wucin gadi ta mulkin soji a ranar Litinin ɗin nan alúmar ƙasar Bangladesh zasu kaɗa ƙuriár zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisun dokoki.

Manyan yan takara biyu waɗanda zasu fafata a zaɓen su ne Sheikh Hasina ta jamíyar Awami League da kuma Khalida Zia yar takarar jamíyar BNP. Waɗannan mata biyu waɗanda dukkanin su sun taɓa riƙe muƙamin Firaminista a Bangladesh sun kwashe kusan shekaru Ashirin suna taka rawa a fagen siyasar ƙasar. Wannan zaɓe dai ana fatan zai kawo ƙarshen mulkin soji waɗanda suka karɓe ragama domin ceto ƙasar bayan da ta faɗa cikin badaƙalar siyasa da rigingimu waɗanda suka tsayar da alámura cik a ƙasar a wancan lokaci.


A ta bakin manjo janar mai ritaya Munirusman yace komawar Pakistan ga mulkin dimokraɗiya abin farin ciki ne. " Yace Bangladesh zata koma kan tafarkin dimokraɗiya bayan tsaiko na shekaru biyu ƙarkashin gwamnatin wucin gadi, to amma yadda ƙasar zata koma kan wannan turba cikin girma da arziki yana da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ƙasar Bangladesh dama kuma yankin baki ɗaya".


A yanzu dai komai ya kammala abin da ake jira kawai shine lokacin zaɓe. Sojoji da yan sanda 50,000 aka baza a ko ina a cibiyoyi da rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar domin tabbatar da cikakken tsaro don kare maguɗin zaɓe da kawar da dukkan wani yunƙuri na taáddanci.


Yayin da ake lale marhabun da wannan zaɓe domin gusawar sojoji daga karagar mulki, a cewar wani manzarcin alámuran siyasa a Bangladesh Ishaq Ahmed yace sojojin na gudun tonon silili ne kawai shi yasa zasu miƙa mulki. A lokacin da ta karɓi mulki gwamnatin riƙon ƙwaryar ta yi alƙawarin tsabtace harkokin siyasa daga taɓargazar cin hanci da rashawa, amma sai mai dokar barci ya ɓige da gyangyaɗi. A shekaru biyu da suka wuce dukkan manufofi da gwamnatin wucin gadin ta soji ta aiwatar, basu taɓuka komai ba sai koma bayan tattalin arziki kuma dukkan kurarin da suka yi na yaƙi da cin hanci, da yawa daga cikin manyan sojojin suma abin da suka aikata kenan. Sai dai kuma a waje guda wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a kwamitin sa ido kan zaɓen Francis Vendrell yace yayi amanna an cimma buri. " Yace Ina tsammanin an sami cigaba mai maána, yanayin wannan zaɓe ya banbanta dana shekarun baya kuma ina gani jamaá sun gamsu da hakan".


Dukkan wanda zai yi nasara a wannan zaɓe ko dai a matsayin jamíya guda ko kuma haɗin gwiwa da sauran jamiyu, wajibi ne ɗan takara ya sami aƙalla kujeru 151 daga cikin adadin kujeru 300 da ake dasu a majalisar dokokin tarayyar. Manazarta dai na ganin cewa jamíyar Awami League ta Shikh Hasina ita ce zata lashe zaɓen.