1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen yan majalisun dokoki a Benin

April 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuOW

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta a jamhuriya Benin,ta fara bayyanan sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki da su ka gudana jiya asabar, a fadin ƙasar baki ɗaya.

A jimilce, saɓanin tunanin da dama, daga jama´ar ƙasa zaɓen ya wakana lami lafia.

A wasu wuraren, kamar Porto Novo babban birnin ƙasar, saida hukumar zaɓe ta ƙara lokaci,domin cike giɓin ɗan jikirin da a samu, wajen buɗa runfunan zaɓen.

Baki ɗaya, kimanin mutane milion 4 ne, ya cencenta su kaɗa ƙuri´a, domin zaɓen yan majalisa 83, daga jerin yan takara 2.158, da su ka hito daga jam´iyun siyasa 24.

Masu sa ido na cikin gida, da na ƙetare, kimanin 200, sun shaidi cewar zaɓen ya wakana lami lafia.