1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

160409 Indien Wahlen

April 16, 2009

Zaɓe a ƙasar Indiya: Fiye da indiyawa miliyan ɗari bakwai ya cencenta su kaɗa ƙuri´a

https://p.dw.com/p/HYNb
Indiyawa sun fara zaɓe a yauHoto: AP

Yau ne al´umar ƙasar Indiya ke fara zaɓen ´yan majalisun dokoki.

A ƙalla mutane miliyan ɗari bakawi ne ya cencenta su fara kaɗa ƙuri´a daga yau, har zuwa 13 ga wata mai kamawa.

Ƙasar Indiya da ake wa taken babbar demokraɗiya ta duniya na da jimlar mutane miliyan dubu ɗaya da miliyan ɗari.

Miliyan ɗari bawai daga cikin su zasu kaɗa ƙuri´a domin tatance ´yan majalisa 543, wanda zasu wakilci jihohi 35 da ƙasar ta ƙunsa a Majalisar Dokoki.

Masu kula da tafiyar harakokin siyasa a ƙasar Indiya na hasashen cewar jam´iyar Congres dake rike da ragamar mulki da Soniya Ghandi ke jagoranta da kuma babban jam´iyar adawa ta Lal Krishna Advani zasu taka rawar gani, to saidai basu iya cimma nasara girka gwamnati ba, tare da sun nemi ƙawance ba, da wasu ƙarin jam´yiu.

A cewar Narasimba Rao wani manazarci akan harakokin siyasar Indiya mazan dawuri, kamar su Gandi da Neru na da babban angizo, a fagen siyasar ƙasar mussamman a jam´iyar Congres Parti dake kan mulki:

Zuri´ar Gandi na da angizo mai tasiri a harakokin siyasar Indiya a tunanina, badan darajar Gandi ba, da zuri´arsa, da tuni!! mutuncin jam´iyar Congres ya zube fiye da yadda yake yanzu, to amma mutanen Indiya sun riƙe amana Gandi, kuma wanan daraja ce jam´iyar ke ciki.

A lokacin yaƙin neman zaɓe jam´iyar Congres tayi dogaro da nasarori iri iri da tace ta samu, ta fannin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma kyautata rayuwar jama´a.

Ƙiddidar gwamnati ta bayyana cewar, an samu cigaba na kusan kashi tara cikin ɗari.

Bugu da ƙari gwamnati ta shiga yunƙurin tattanawa da kashe duniya mussaman Amurika da Pakistan da zumar samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A nata gefe, jam´iyar BJP mai adawa tayi shelar wanzar da wasu sabin hanyoyin na ingata rayuwa, da zaran jama´ar ƙasa suka bata damar hawa kan karagar mulki.

Shugaban wannan jam´iya, LK Advani yayi zargi da kakkausar halshe irin yadda hukumomi ke nuna sassauci ga matakan tsaron ƙasa, wanda suka yi sanadiyar kai hare haren da suka rutsa da birnin Mumbai.

To saidai a cewar Narasimba Rao duk wannan kalamomi daga ɓangarorin biyu farfagan da ne kawai:

Abunda zai tasiri a wannan zaɓe shine rawar da tsakatsakiyar jam´ iyu zasu iya takawa.

Ɗaya daga cikin wannan jam´iyun itace ta Mayawati, gwamnan Uttar Pradesh.Ranar 16 ga watan Mayu za a bayyana sakamakon zaɓen baki ɗaya, duk gwamnatin da ta hau zata ci karo da mahimman matsalolin da Indiyawa ke kuka da su, wanda suka hada da cin hanci, da rashawa da kuma taɓarɓarewar tsaro.

Mawallafi: Matthay/ Yahouza Sadissou

Edita: Umaru Aliyu