1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen ´yan Majalisun Dokoki a Indonesiya

April 9, 2009

Tara ga watan Afrilu: ranar zaɓen ´yan Majalisun Dokoki a Indonesiya

https://p.dw.com/p/HTO1
Zaɓe a IndonesiyaHoto: AP

Tara ga watan Afrilu, al´umar ƙasar Indonesiya ke zaɓen´yan majalisun dokoki, wanda a sakamakon sa , mutane fiye da miliyan 170 da suka cencenci kaɗa ƙuri´a zasu zaɓen´yan majalisun dokokin 560.

Cimma nasara shirya zaɓen na Indonesiya dake matsayin ƙasa mafi yawan musulmi a duniya, na mtasayin wani babban ƙalubale ga hukumar zaɓe mai zaman kanta.

Ƙasar Indonesiya na da jimlar mutane miliyan ɗari bakwai, dake zaune a cikin tsibirrai fiye da dubu 17.

Mutane miliyan 170 da ya cencenta suka ƙuri´a a wannan zaɓe za su tantance mutane 560 da zasu zama ´yan majalisa daga jimlar dubunnan ´yan takara .

Jam´iyun siyasa 38, wanda suka haɗa da PD ta shugaban Ƙasa Susilo Bambang Yudhyono suka ajje ´yan takara a wannan zaɓe.

Kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada, duk jam´iyar da ta samu ƙasa ga kashi 2, 5 cikin ɗari na jimlar ƙuri´un da aka kaɗa, ba zata samu kujera a Majalisa ba.

A wani mataki na riga kafi ga abkuwar tashe tashen hankulla, hukumar zaɓe ta dakatar da yaƙin neman zaɓe kwanaki ukku kamin ranar zaɓen.

A lokacin da aka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe, a tsakiysar watan Maris da ya gabata, shugaban ƙasa Susilo Bambang Yudhoyono, yayi kira ga jama´a da cewa kowa ya nuna halayen dattako, ta yadda komi zai wakana lau lami.

Ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a ta nunar da cewa, jam´iyar PD ta shugaban ƙasa na da alamun taka kyakkyawar rawa a wannan zaɓe.

An girka jam´iyar PD a shekara ta 2001, kuma ya samu kashi 7,5 cikin ɗari na ƙuri´un da aka jefa, a zaɓen shekara ta 2004.

A watan Maris da ya wuce, hukumar bincike ta LSI, ta hango cewar, jam´iyar PD a wannan karo, zata zo sahu gaba, tare da kashi 24,3 cikin ɗari na yawan ƙuri´u, sai kuma jam´iyar PDIP ta tsofan shugaban ƙasa wadda zata zo sahu na biyu, tare da kashi 17,3 cikin ɗari.Ra´ayin na baya fage ya gano cewar jam´iyar Golkar ta mataimakin shugaban ƙasa Jusuf Kalla zata zo ta ukku.

To saidai fa ba a san maci tuwo ba, sai miya ta ƙare domin fiye da kashi 20 cikin ɗari na jama´a basu bayyana ra´ayoyinsu ba.

Kazalika, babu tabbas a game da sha´anin zaɓe a Indonesiya.

Tunni dai jam´iyun siyasa sun fara tattanawa domin kafa gama ƙarfi to saidai ba a san abunda wannan tattanawa zata haifar ba kamar yadda Alfan Alfian wani mai sharhi akan harkokin siyasa ya nunar:

Babu wata aƙida da jam´yun ke yin dogaro da ita wajen ƙulla ƙawancen.Saidai akwai ƙwarori daga shugabani dake aiki da manufofin jam´iyunsu, kuma akasari mutane ne masu angizo a cikin fagen siyasa.A nan jam´iyun siyasa tamkar sarautar gargajiya ce, abunda shugabani ke so shi ake aikatawa.Saboda haka ba a yanke ƙauna a game da ko wane irin ƙawance.

Sakamakon zaɓen ´yan majalisun dokokin, shine zai ƙayyade ´yan takara da zasu shiga zaɓen shugaban ƙasa na ranar 8 ga watan Juli a wannan shekara.Jam´iya ko kuma rukunin jam´iyun da suka sami a ƙalla kashi 25 cikin ɗari na ƙuri´un da aka shefa a zaɓen ´yan majalisa, kokuma suka mallaki kashi 20 cikin ɗari na ´yan majalisa ke da damar ajje ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.

Edita:Abba Bashir