1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen yan majalisun dokoki a Senegal

June 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuJs

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a ƙasar Senegal, na ci gaba da tattara sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki da ya wakana jiya lahadi, a fadin ƙasar baki ɗaya.

Saidai rahottani daga Dakar babban birnin Senegal, sun ruwaito cewar, zaɓen bai samu karɓuwa ba, dalili da ƙaurace masa, da jama´iyun adawa su ka yi.

Jam´iyar PDS mai riƙe da ragamar mulki, ta shugaba Abdullahi Wade, tare da yan tsirarun jam´iyu, masu goya mata baya, su kaɗai su ka yi kiɗin su , su ka kuma taka rawar su.

Ja´iyun adawa fiye da 10, sun yanke shawara ƙauracewa zaɓen a dalili da abun da su ka kira murɗiya da a ka tanadi shiryawa, da zumar baiwa jam´iyar PDS gagaramin rinjaye a majalisar dokoki.

Wanda su ka sa ido ga wannan zaɓe sun nunar da cewar bai yi amarshi ba ko mici ƙala zaratin, abinda ke matsayin koma baya, ga demokradiya a Senegal, ƙasar da ake ɗauka tamkar zakaran gwajin dafi, a nahiyar Afrika, ta fannin girkuwar tsarin mulkin demokraɗiya.