1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300809 Deutschland Wahlen

August 31, 2009

Manyan jam´iyun Jamus sun samu koma baya a zaɓen majalisun dokoki uku na ƙasar

https://p.dw.com/p/JMdH
Shugabar gwamnati Angela MerkelHoto: AP

A yayin da ya rage makonni huɗu a gudanar da man'yan zaɓukan ƙasar Jamus, babban abokin hamayyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ya yi ikirarin cewar, zai sami nasara a zaɓukan da za'a yi, bayan koma bayan da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin ta samu a zaɓukan da aka yi a wasu jihohin ƙasar.

Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta shiga cikin halin rashin tabbas a wannan litinin bayan rasa rinjayen da take dashi a wasu jihohi biyu daga cikin jihohi ukkun da aka gudanar zaɓuka a wannan lahadin, inda Sakataren Janar na jam'iyyar Social Democrats Hubertus Heil kuma ke cewar, tilas ne a dama da jam'iyyarsa cikin duk wani ƙawancen jam'iyyun da zasu yi mulki a jihohin biyu, idan aka yi la'akari da rawar data taka.

A da dai jam'iyyar CDU ce ke da gagarumin rinjaye a jihohin Saarland da Thuringia - matsayin da a yanzu ya kau, domin idan aka kwatanta da zaɓukan shekaru biyar da suka gabata, to, a yanzu ta sami koma baya da kashi goma sha ukku cikin ɗari ne a jihar SaarLand, kana ta rasa rinjayen kimanin kashi goma sha ɗaya cikin ɗari a jihar Thuringia. Sai dai koma bayan da ita CDUn ta samu a jihar Saxony bata kai ko da kashi ɗaya cikin ɗari ba.

Duk da wannan halin da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sami kanta a ciki, mai tafiyar da harkokin jam'iyyar Norbert Röttgen, ya ce yana da cikakken fatan kai labari:

"Idan jam'iyyar CDU bata da isasshen ƙarfi, kenan babu tabbaci, kuma Jamus tana buƙatar tabbaci a game da halin da ake ciki. Jam'iyyar CDU tana da ƙarfi, wannan shi ne abinda aka nuna."

Ko da shike sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya bayannan da aka yi, ya nuna cewar, jam'iyyar SPD, nada kashi ashirin da ukku ne cikin ɗari - idan aka kwatanta da CDU, wadda keda kashi talatin da bakwai cikin ɗari, ɗan takarar shugaban gwamnatin Jamus a ƙarƙashin jam'iyyar SPDn, Farank Walter Steinmeir, wanda kuma ke riƙe da muƙaman mataimakin shugabar gwamnati a yanzu, da kuma Ministan kula da harkokin wajen ƙasar, ya ce, waɗanda ke cewar, tuni masu zaɓe suka yanke shawara game da yadda zata kaya a man'yan zaɓukan ƙasar, sunyi kuskure, bisa la'akari da sakamakon da aka samu a zaɓukan jihohi ukkun. Seinmeir ya furta hakanne a jawabin da ya yiwa magoya bayansa:

"Wannan zaɓe ya yi kyau ga jam'iyyar SPD. CDU ta yi hasarar wuraren da dama, wannan ya nuna cewar ƙasar nan bata ƙaunar gamayyar Christian Democrats da 'Yan Liberals"

A nasu ɓangaren, wasu Jaridun ƙasar Jamus, sun yi gargaɗin cewar, lokaci bai yi ba, da Steinmeir zai fara nuna cikakken fata ga zaɓukan. A cewar jaridar harkokin kasuwanci ta Handelsblatt, ba za'a iya yin anfani da sakamakon zaɓukan ranar lahadinnan a matsayin mizanin yin hasashen yadda sakamakon zaɓukan tarayya zasu kasance ba. A ranar ashirin da bakwai ga watan Satubarnanne - idan Allah ya kaimu za'a gudanar da man'yan zaɓuka a nan Jamus.

Mawallafa: Nina werkhäuser/Saleh Umar Saleh

Edita: Mohammad Nasiru Awal