1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a ci gaba da zanga-zanga a Zimbabuwe

Abdul-raheem HassanSeptember 12, 2016

'Yan adawa sun ce za su cigaba da yin zanga-zanga duk kuwa da hani da 'yan sanda suka yi a kasar bayan da suka fitar da wata doka kan wannan batu.

https://p.dw.com/p/1K0tG
Simbabwe Harare Proteste gegen Präsident Mugabe
Hoto: picture-alliance/AA

'yan adawa a Zimbabuwe sun kuduri aniyar ci gaba da gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar. A karshen makon da ke tafe ne 'yan adawar ke shirin gudanar da gangamin kalubalantar hukumar zaben kasar a gabannin zabubbukan shekara ta 2018. Jam'iyyu 18 ne dai suka yi gamayyar kyamatar halayyan hukumar zaben da su ke ganin akwai nuna son kai da alamar marawa shugaban kasar Robert Mugabe baya.

To sai dai jam'iyun adawa a kasar na son yin amfani damar wannan zanga-zanga da nufin jan hankalin kasa da kasa da wakilan Majalisar Dinkin Duniya wajen sanya idanun a zaben kasar nan gaba. Wannan dai na zuwa ne makonnin kadan bayan da 'yan adawar su ka shirya wata zanga-zangar da ta rikede zuwa tashin hankali wanda ya yi jawo 'yan sanda suka yi ta fesa hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar da suka mamaye Harare babban birnin kasar.