1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar wanda ake zargi da kai hari a Faransa

Zulaiha Abubakar MNA
February 5, 2018

Salah Abdeslam dan asalin kasar Maroko, Faransa na zarginsa da hannu a mummunan harin da yayi sanadiyyar rayukan mutane 130 a 2015.

https://p.dw.com/p/2s7r5
Belgien Prozess Salah Abdeslam in Brüssel
Hoto: picture-alliance/AA/D. Aydemir

Salah Abdeslam mutumin da ya yi saura daga cikin mutanen da kasar Faransa ke zargi da kai wani mummunan hari a kasar a shekara ta 2015 ya bar gidan kurkukun da ake tsare da shi zuwa Brussels inda za a fara shari'arsa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Sanarwar ta kara da cewar an ga  jerin gwanon motocin 'yan sanda sun fita daga gidan yarin Fleury-Merogis da ke wajen birnin Paris da misalin karfe 4 na asubahin wannan Litinin duk kuwa da cewar ba za a iya tantance adadin mutanen da ke cikin motocin ba.

Shi dai wanda ake zargin an haife shi ne a shekara ta 1989 dan asalin kasar Maroko wanda kasar Faransa ta yi zargin yana da hannu cikin kai mummunan harin da yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane 130 tare da jikkata wasu 368.