1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a gurfanar da Pfizer gaban kotu

July 2, 2010

Kotun ƙoli ta Amirka ta share hanyar ɗaukaka ƙara kan kamfanin Pfizer a ƙasar

https://p.dw.com/p/O9FM
Bikin cikar shekaru 50 da 'yancin kan ƙasar KongoHoto: AP

Da farko dai zamu fara ya da zango ne a janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo, wadda a wannan makon tayi bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kanta. A lokacin da take ba da nata rahoton jaridar Frakfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Yau shekaru hamsin bayan samun 'yancin kan ƙasar Kongo, al'amura sun taɓarɓare kwata-kwata, inda matsayin rayuwar al'ummar ƙasar ma ya zama gwamma jiya da yau. Ana ci gaba da take haƙƙin ɗan-Adam da kashe-kashe na gilla kuma ƙurar rikici har yau ba ta lafa sosai ba a ƙasar ta ƙuryar tsakiyar Afirka, wadda Allah Ya fuwace mata ɗimbim arziƙi."

Bisa ga dukkan alamu kamfanin harhaɗa magunguna na Pfizer zai fuskanci ƙara a kotu domin biyan diyyar dubban miliyoyin dalar Amirka sakamakon gabatar da magungunan da yayi ba a bisa ƙa'ida ba inda mutane da dama suka halaka, a baya ga waɗanda suka samu illa a ƙwaƙwalwa ko makanta. Jaridar Die Welt ta duba matsalar inda take cewa:

"Wannan shari'a in har an gabatar da shi a Amirka kamfanin Pfizer zai fuskanci barazanar gaske. Domin kuwa a baya ga diyyar dubban miliyoyin dala kotuna a Amirka na da ikon cinsa tarar kuɗi. Bugu da ƙari kuma zargin da ake wa kamfanin yana da munin gaske ta yadda zai zubar da martabarsa a idanun duniya muddin kotun da zata yi shari'ar ta tabbatar da laifin da ake zargin kamfanin na Pfizer da aikatawa. Ba ma a Amirka kaɗai ba, hatta a nan Jamus doka bata amince a gwada ƙwayar magani akan majiyyaci ba tare da yardarsa ba. An kuma ma haramta gwada magani akan yara ƙanana."

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi nazari akan matsalar ta Pfizer, inda ta ce a sakamakon irin munanan abubuwan da suka biyu bayan gwaje-gwajen magunguna akan yara ƙanana da kamfanin na Pfizer yayi a Nijeriya, kotun ƙoli ta Amirka ke ba wa dangin waɗanda lamarin ya shafa goyan baya. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Akwai kamfanonin harhaɗa magunguna da dama na ƙasashe masu arziƙin masana'antu kan gwada magungunansu ne a ƙasashe masu tasowa saboda ƙarancin majiyyatar dake yarda a gwada magunguna akansu a ƙasashe masu arziƙin masana'antun. Bugu da ƙari kuma gwaje-gwajen magungunan a ƙasashe masu tasowa ya fi sauri da rahusa, kuma a nan ne take ƙasa tana dabo, saboda galibi majiyyatan ba su da wata masaniya a game da waɗannan gwaje-gwaje da ire-iren abubuwan da ka iya biyowa baya."

Ɗaya daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu dangane da cimma burin Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da shekarun dubu biyu shi ne ƙarancin jami'an kiwon lafiya musamman ma a nahiyar Afirka a cewar jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ce:

"Dalilin haka shi ne da yawa daga cikin waɗannan manufofin suna da danganta da kiwon lafiya, amma a sakamakon ƙarancin likitoci da wuya kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu. Misali dai ƙasar Muzambik mai yawan mutane miliyan ashirin da biyu amma duka-duka yawan likitoci a duk faɗin ƙasar bai zarce ɗari biyar da arba'in da takwas ba. Kazalika ma ƙasar Nijer, wadda ke da yawan jama'a miliyan goma sha huɗu, amma duka-duka likitocinta ba su wuce metan da tamanin da takwas ba. Kai Liberiya ma gaba ɗayanta yawan likitocinta ba su wuce hamsin da ɗaya ba, a saboda haka manufar ƙayyade yawan mace-macen mata masu haifuwa da yara ƙanana ya zama tamkar ba'a."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu