1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Nijar

Salissou BoukariFebruary 26, 2016

Sakamakon karshe da hukumar zaben Nijar CENI ta bayyana, ya nunar cewa za a je zagaye na biyu tsakanin Shugaba mai ci da Hama Amadou da ke tsare a gidan kaso.

https://p.dw.com/p/1I3Ae
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Issoufou Mahamadou da Hama Amadou a 2011Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zaben kasar ta bayyana da yammacin wannan Jumma'a ya nunar cewar za a je a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Alhaji Issoufou Mahamadou da kuma dan takarar jam'iyyar Moden Lumana Afirka Malam Hama Amdou. Sakamaon da hukumar ta CENI ta bayyana, dan takarar jam'iyyar ta PNDS Tarayya mai mukli wanda ya sha alwashin yin bugo daya na kawo wukka tun a zagayen farko ya samu kashi 48,41% a yayin da Hama Amadou dan takarar da yanzu haka ke tsare a gidan kurkuku ya samu da kashi 17.69% daga cikin dari na kuri'u kimanin miliyan bakwai da rabi da aka kada.

Tuni dai dama jam'iyyun adawar ta Nijar suka kulla wani kawance mai suna COPA da nufin kama wa dan takarar da zai zo a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar wanda za a shirya a ranar 20 ga watan Maris mai zuwa. A yanzu dai abin jira a gani shi ne ko in har wannan kawance zai ci gaba da kasancewa a dunkule domin kuwa wannan ba shi ne karo na farko ba a siyasar Nijar da wasu jam'iyyu ke kulla kawance da nufin tafiya tare amma daga bisani yake watsewa.