1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

za a karrama wasu mutane bisa namijin kokarin da suka yi

ibrahim saniSeptember 29, 2005

Hukumar rights livelihood ta yanke hukuncin karrama wasu bayin Allah, ko shin su wanene....

https://p.dw.com/p/BvZJ
Hoto: AP

A gaba daya dai a cewar rahotanni da suka iso mana kasashe 77 ne suka gabatar da yan takarar su don neman wannan lambar yabo daga kasashe 39 na duniya.

Bugu da kari rahotannin sun tabbatar da cewa mutane hudu sun fito ne daga nahiyar Africa hudu kuma daga kasashen larabawa,mutane ashirin kuma daga yankin Asia, kana daya kuma daga kasar Australia. Ragowar sun hadar da 26 daga nahiyar turai, guda goma sha biyu kuma daga latin Amurka kana a karshe goma suka fito daga arewacin America.

A yayin da wannan hukuma ta Right Livelihood ta karbi sunayen wadan nan mutane sai tayi zube ban kwarya ta don zabar mutanen da suka fi cancanta a basu wannan lamba ta yabo ta girmamawa da kuma karfafa gwiwa.

Bayan da aka gudanar da wannan taron ne sai aka zabo mutane irin su Mr Francisco Toledo wanda dan kasar Mexico ne.

Alkalan wannan hukuma ta Livelihood sun shaidar da cewa sun zabo wannan mutumin ne bisa irin namijin kokarin daya nuna wajen ta´allaka ilimin daya samu na zane zane ga zane zanen abubuwa da zasu taimakawa wajen kare muhalli da kuma al,ada ta alummomin yankin sa dake Oaxaca.

Akwai kuma Mr Maude Barlow da abokin sa wato Tony Clarke, wayanda yan kasar Canada ne. Su kuma an zabo sune bisa irin kokarin da suke wajen ganin an gudanar da adalci da kuma kare hakkin yadda ake amfani da ruwa, wanda hausawa kance abokin aiki.

A dai tsarin sunayen ba a bar mata ba, domin kuwa akwai Irene Fernandez daga Malasia.Ita kuma ta shahara ne game da fafutikar kare hakkin mata da kuma baki maikata dake balaguro daga kasa izuwa wata kasar.

Haka kuma akwai Roy Sesana daga itama kuma daga Botswana. Ita kuma tayi suna ne akan ganin alummomin yankin ta sun martaba al,adar kaka da kakanni da suka gada.

Wannan hukuma dai ta Rights Livelihood an kirkiro tane a shekara ta 1980,don karrama mutane da suka yi fice a fannonin da alummomin su ke bukatar taimakon gaggawa kana a hannu daya kuma da dimbin kalubalen dake addabar su.

Wannan dai lambar yabo ta right livelihood na a na kusa da matsayin lambar yabo ce ta zaman lafiya ta Nobel. Ya zuwa yanzu an kiyasta cewa mutane sama da 100 ne daga kasashe 48 na duniya suka karbi wannan lamba ta yabo.

Ana dai bayar da lambar wannan yabon ne a majalisar dokoki ta kasar Swedin a kowace shekara ta Allah, ta´ala

Bayanai dai sun shaidar da cewa za a gudanar da taron manema labarai na wadan nan mutane da muka ambata a can birnin stockholm ranar 7 ga watan disamba na wannan shekara da muke ciki, kana a ranar 9 ga wata kuma a mika musu wannan kyautar lambar yabon.