1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a shirya sabon zaɓe a ƙasar Kirgistan

April 22, 2010

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Kirgistan ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen 'yan majalisa goma ga watan Oktoba

https://p.dw.com/p/N2gF
Shugabar gwamnatin riƙon ƙwarya ta KirgistanHoto: AP

Gwamnatin riƙon kwarya a ƙasar Kirgistan ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen yan majalisar dokoki a ranar goma ga watan Oktoba mai zuwa, mataimakin friministan ƙasar Oumourbek Tekbaiev ya sheda cewa suna sa ran za a' game zaɓen yan majalisar da na shugaban ƙasa,sannan a cikin watan Yuni mai zuwa a gudanar da ƙuria'a jin ra'ayoyin jama'a akan kawo koskorima ga kundin tsarin mulki na ƙasar.Gwamnatin dai ta riƙon ƙwarya ta ce itace ke da cikkaken iko da mulki  sannan kuma ta yi watsi da kallamun da hamɓararen shugaban  mista Bakiev ya baiyana daga ƙasar Belarusiya inda ya ke gudun hijira cewa haryanzu shine cikkaken shugaba na Kirgistan.

Mawallafi  : Abdourahamane Hassane

Edita         : Yahouza Sadissou  Madobi