1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi taron ƙoli kan ƙasar Côte d’Ivoire.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buru

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan zai halarci wani taron ƙoli a ƙasar Côte d’Ivoire a ran laraba mai zuwa, inda zai yi shawarwari da shugabannin ƙasashen Afirka Ta Yamma da kuma na Côte d’Ivoire ɗin, Laurent Gbagbo, don tabbatad da cewa an kammala shirye-shiryen zaɓen ƙasar da za a gudanar a cikin watan Oktoba mai zuwa.

Tun cikin shekara ta 2002 ne dai, ƙasar Côte d’Ivoire ɗin ta rabu a sassa biyu, wato yankunan arewaci da kuma kudancin ƙasar, bayan wani gajeren yaƙin basasan da aka gwabza. A yunƙurin sake haɗe ƙasar ne kuwa, aka shirya gudanad da zaɓe a ran 31 ga watan Oktoba. Amma har ila yau, ana tafiyar hawainiya wajen kammala duk shirye-shiryen da aka tsara kafin ranar zaɓen. Ɓangarorin da aka fi huskantar matsala a kansu a halin yanzu dai sun haɗa ne da kwance wa mayaƙan ɓangarorin biyu ɗamara da kuma tsarin tabbatad da asalin masu ka da ƙuri’un.

Shugabannin ƙasashen Afirka Ta Yamma da su ma za su halarci taron sun haɗa ne da na Najeriya, da Ghana, da Nijer, da Burkina Faso, da kuma shugaban Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Afirka, Alfa Omar Konare.