1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi zaɓen Najeriya a farkon shekarar 2011

July 22, 2010

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da gudanar da zaɓe a cikin watan Janeru

https://p.dw.com/p/ORvU
Masu zanga-zangar neman a yiwa tsarin zaɓen Najeriya gyaran fuskaHoto: AP

Majalisar dattawan Najeriya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da shirya zaɓukan ƙasar a cikin watan Janerun shekara mai zuwa, a wani abin da ke zama matsin lamba ga jam'iyar PDP dake janragamar mulki ƙarƙashin shugaba Goodluck Jonathan da ta warware rarrabuwar kawuna dake tsakanin 'ya'yanta. To sai dai dole sai ita ma majalisar wakilai ta amince da sabbin dokokin zaɓen bayan da a jiya Laraba majalisar dattawa ta yanke shawarar canza kundin tsarin mulki domin share fagen gudanar da zaɓen a cikin watan Janeru. A wannan Alhamis an jiyo shugaban hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta wato INEC, Farfesa Attahiru Jega na cewa lokacin da za a iya gudanar da zaɓukan shi ne tsakanin 8 zuwa 15 ga watan na Janeru idan aka tabbatar da kwaskwarimar da aka yiwa kundin tsarin mulkin. To sai dai kuma ya ce ƙarancin kuɗi ka iya zamewa hukumarsa alaƙaƙai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar