1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a binciki sojojin Najeriya

Abdul-raheem Hassan
September 11, 2017

Kwamitin da shugaban Najeriya ya kafa don jin ba'asin take hakin jama’a da ake zargin sojoji ya fara zamansa a Abuja.

https://p.dw.com/p/2jkSy
Nigerianische Rebellen Niger Delta
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Dimbin zarge-zargen take hakin jama'a da ake wa sojojin Najeriyar da aka gabatar sun raja'a akan batun wuce iyaka da ake yiwa sojojin a ayyukan da suka yi a shekarun baya, duk da cewa batun zargi na rawar da suka taka a kan aiyyukan ta'adanci ya fi daukan hankalin jama'a. Farfesa Jibrin Ibrahim na cin 'yan kwamitin da ke sauraron koke koken al'umma.

Tschad Armee Soldaten Zeremonie
Sojojin NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

"Mu zamuyi aikin da akace muyi, a saurari mutanennan kasannan a tabbatar ko gaskiyane ko ba gaskiyabane. Mu fadi abubawan da ya kamata gwamnati ta yi, shugaban kasa lokacin da ya kafamu, ya ce indai mukayi aikin yadda ya kamata, to abubuwan da mukace gwamnati za ta aiki da shi, muna fata hakan zai faru."

Kwamitin dai ya fara ne da sauraren ba'asin zargin cin zarfain alummar Moo Valley da ke jihar Benue wadan da ke zargin sojojin Najeriya da tada mutanen daga yankunan su ba tare da shiri ba. Ogbeni Gbola Oyebano shi ne lauya da ke wakiltar rundunar sojojin kasar, yace:

"Zargi dai ai zargi ne har sai an tabbatar da shi ya ke zama laifi, bisa ga wannan batu, saboda haka zargin da ake yiwa rundunar sojan Najeriya za'a gane a binciken da ake gudanarwa , amma zan iya cewa ba su da laifi a kan wannan, kuma a karshe za'a tabbatar da hakan.''

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Yan kungiyar Shi'a a NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

To sai dai kungiyar ‘yan Shi'a da ta dade tana takun saka da rundunar sojin kasar a kan abinda ta kira musgunawa wasu mambobin kungiyar da ke a fadin kasar, ta kauracewa zaman sauraren jin ba'asin.

Nigeria Taraba staat Kinder
Hoto: Picture alliance/dpa/epa/G. Esiri

Kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International sun hallarci zaman, tare da bayyana abinda suke fatan ganin a karshen binciken. Malam Isah Sanusi shi ne jami'in yada labaran kungiyar.

"Duk mutumin da yake da matsala ta take ahkkin bil'adama a Najeriya bukatar sa bata wuce adalci, amma ansha yin irin wadannan kwamitoci amma kwalliya bata biyan kudin sabulu. Mu dai muna bawa kwamitin kyakkyawar fata."

Yan Najeriya na sa idon ganin ko gwamnatin zata iya aiwatar da sakamakon kwamitin kamar yadda ta yi alkawari musamman ladabtar da duk wani mai laifi, abinda zai bambanta wannan bincike da wadnada aka yi a baya, inda rundunar sojan Najeriyar ta wanke kanta daga duk wani zargi.