1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a gana ido da ido tsakanin Bush da Putin a zauren taron G8

June 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuJa
An shiga kwana na biyu a taron koli kasashen kungiyar G8 dake gudana a Heiligendamm a nan Jamus, inda ake sa ran yin wata tattaunawa mai zafi tsakanin shugaban Amirka GWB da shugaban Rasha Vladimir Putin. A cikin watannin baya-bayan nan dai Putin ya yi ta saka ayar tambaya game da shirin Amirka na kafa sansanin kakkabo makamai masu linzami a Turai. A nasa bangaren ana sa rai Bush zai nanata zargin da yake yi cewa ana fuskantar tafiyar hawainiya a sauye sauyen demukiradiya a Rasha. Bush ya ce yana farin ciki dangane da tattaunawar da zai yi da Putin.