1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a gana tsakanin Bush da Abbas a birnin New York

September 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuAl

A ranar litinin mai zuwa shugaban Amirka GWB zai gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a gefen taron babbar mashawartar MDD a birnin New York. Wani kakakin fadar White House ya ce shugabannin biyu zasu tattauna akan batun maslahar nan ta kasashe biyu don warware rikicin yankin GTT. Ba a dai sani ba ko Bush zai kuma gana da FM Isra´ila Ehud Olmert a New York. Wannan sanarwa ta biyo bayan jerin shawarwari ne da aka yi a wannan makon tsakanin sakatariyar harkokin wajen Amirka C.-Rice da shugaba Abbas da kuma FM Olmert akan shirye shiryen babban taron samar da zaman lafiya wanda Amirka zata dauki nauyin gudanarwa a karshen wannan shekara. Misis Rice ta tabbatarwa shugaba Abbas cewa taron zai kuma mayar da hankali a dangane da kafa wata ´yantacciyar kasar Falasdinu.