1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a katse shawarwari tsakanin EU da Iran akan shirinta na nukiliya

October 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bug0

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce zata dakatar da tattaunawar da take yi da Iran akan shirinta na nukiliya da ake takaddama akai. Wani jami´in diplomasiya a birnin Brusels ya fada cewa ministocin harkokin wajen kungiyar ta EU zasu gana a Luxemburg a ranar talata mai zuwa inda a hukumance zasu ayyana katse zama shawarwarin da Iran wanda suka ce bai haifar da wani sakamako ba. Ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier ya tofa albarkacin bakinsa a kan wannan batu yana mai cewa.

“Abin da ke faruwa a yanzu shi ne da farko ba zamu koma kan teburin shawarwarin ba. Saboda haka babu wani dalili da zai sa a hana kwamitin sulhu yin zama na musamman akan batun. Ba wani abin boyo a nan musamman dangane da matakin farko na sanyawa Iran takunkumi. Na biyu kuma shine taron ministocin harkokin wajen EU a London ya nunar da cewa hakan ba shi ne karshen kokarin warware wannan rikici ta hanya diplomasiya ba.”