1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a rufe sansanin baƙin haure na Lampedusa

December 22, 2009

Mahukuntan ƙasar Italiya sun ƙuduri anniyar rufe sansanin baƙin haure mafi girma a Turai

https://p.dw.com/p/LAvR
Baƙin haure maƙare cikin jirgin ruwaHoto: DW

Tsibirin Lampedusa dake a ƙasar Italiya ya kasance wani babban sansani, inda mahukuntan ƙasar ta Italiya ke tsugunar da baƙin haure. Yanzu haka sansanin ya cika maƙel kuma a sandiyar haka, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adam su ke zargin mahukuta a Rom, da rashin kula da bil'adama, abinda ya sa yanzu suka shirya rufe sansanin.

Mazauna a wannan sansani dai, sun yi ta bada rahotonni daban daban ta yadda aka ajiyesu ba tare da samar musu gidajen kwana ba. Duk kuwa da irin tsananin sanye da akeyi a turai.

An gudnar da waƙar kiristoci a tsibirin Lampedusa, ministan kula da al'du na ƙasar ta Italiya Antonio Pappalardo yace wannan shine karo na farko da aka rera waƙoƙi a bisa iƙirari na 'yanta mutanen waɗan da ke tsare a Lampedusa, hakan ya na nunin cewa duniya ba ta manta da al'ummomin daban da da suke a tsibirin ba.

Abtransport der Bootsflüchtlinge vom Hafen Lampedusa
Baƙin haure daga AfirkaHoto: DW/Pretersmann

Pappalardo yace."Abon kaito ne ace baƙin haure da dama sun mutu a sandiyar 'yuwa da shututtuka. Duk a cikin koɗoyinsu na isa nahiyar Turai"

Yanzu watanni da dama babu mutanen da ke isowa a wannan sansanin, amma bawai hakan ya na nufin baƙin haure sun daina shigowa kenan ba, kamar yadda Giusy Nicolini, wanda ta yi shekaru da yawa ta na fafitikar kare haƙiin baƙin da ke a wannan tsibirin tace.

"Dayawa sun mutu a kan han'ya, wassu kuma su na kan neman han'yar da sa zu shigo, kuma idan su ka samu dama shigowa za su yi, kana idan har su ka iso to anan gaba ba za'a ajiyesu a sansanin Lampedusa ba, sai dai a maida su inda suka fito. Ga waɗanda su ka nitse a ruwa kuwa babu wanda ya son adadinsu, tinda babu lissafi da akeyi a kansu"

Duk da irin baƙar azabar da baƙin haure ke sha kafin isarsu Turai, amma hakan ba ya karya gwiwar masu shigowa, wato dai ba su ma damu ba, kamar yadda limamin Kirista Don Vincent ya bayyan. "Lampedusa ta kasance wata tasha inda babu abinda mutun ba zai gani ba, akan kama baƙin daga gaɓar tashar jiragen ruwa, daga nan akai su sansanin tsare mutane. Bayan wassu kwanaki a shigo da su nan Italiya. ɗaya daga cikin waɗan ni ne kai na Don Vincent."

Mahukuntan ƙasar dai yanzu sun ɗau tsauraren matakai na hana samun 'yan gudun hijira nan gaba. kamar yadda wannan soja mai sintiri a bakin tekun ƙasar ya bayyana. "Yace yanzu babu wani baƙwon haure ko ɗaya anan, dama an gina wurinne domin mutane huɗu zuwa biyar kawai a matsiyin ko ta kwana idan aka samu wani hatsari, idan ma har wani jirgin ruwan ya sake isowa anan"

Italien Flüchtlinge auf Lampedusa
Baƙin haure a gaɓar tekuHoto: AP

Yanzu haka dai ƙasashen Libiya da Italiya sun ƙulla wata yarjejeniya, wanda za ta hana baƙin haure tsallakowa su shigo turai, ma'ana daga ƙasar ta Libiya za'a maida baƙin kasashensu.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Karl Hoffmann

Edita: Umaru Aliyu