1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a yi zagaye na gaba na taron sulhun lardin Darfur a ran talata mai zuwa

November 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvJ8

A ranar talata mai zuwa za´a koma tattauna batun wanzar da zaman lafiya da nufin kawo karshen rikicin lardin Darfur da yaki ya daidaita a yammacin Sudan. Kakakin kungiyar tarayyar Afirka AU, wato Nuruddin Mezni ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an jinkirta fara zagaye na 7 na shawarwarin yin sulhun da kungiyar ta AU ke daukar nauyin gudanarwa a birnin Abujar Nijeriya. Da farko dai da a gobe litinin aka shirya gudanar da taron. Kakakin ya ce sun samu takarda daga dukkan sassan biyu ta neman a jinkirta taron har sai ranar talata da rana, kuma kungiyar AU ta amince da wannan bukatar. Yanzu haka dai wakilan kungiyoyin ´yan tawaye biyu sun isa birnin na Abuja, sannan a gobe ake sa ran isar tawagar gwamnatin Sudan a babban birnin na tarayyar Nijeriya.