1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a Indonesia---

jamilu saniSeptember 20, 2004

Tsohon janar din sojin Indonesia da ya tsaya takara da shugaba Megawati shine ke kan gaba a zaben shugban kasar da aka gudanar zagaye na biyu yau litinin----

https://p.dw.com/p/BvgK
Hoto: AP

Tsohon janar din sojin kasar Indonesia da yayi alkawarin bulo da matakai na yaki da aiyukan tarzoma tare da bunkasa tattalin arzikin Indonesia matukar dai ya sami nasarar hawa kann kargar mulki,shi aka baiyana a matsayin mutumin da ya sami gagarumar nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar zagaye na biyu inda suka kara da shugaba mai ci a yanzu Megawati Sukarnoputri.

Sulsilo Bambang Yhudhayono ya taba zama ministan tsaron kasar Indonesia a zamanin mulkin Megawati,shi din ne kuma hukumar zaben kasar Indonesia ta ce ya sami kashi 59 daga cikin dari na kuriun da aka kada lokacin da aka gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu yau litinin a kasar Indonesia yayin da ita kuma shubaba mai ci a yanzu Megawati ta sami kashi 41 daga cikin dari na kuriun da aka kada lokacin zabe.

A wani bincike da hadin kann wasu kungiyoyi masu zaman kann su suka yi a dangane da makomar zaben shugaban kasar Indonesia,sun yi hasahen cewar Yudhayono zai sami kashi 61.2 na kuriun da aka kada lokacin zabe,yayin da shugaba Megawati ta sami kashi 38.8 daga cikin dari na kuriun da aka kada a lokacin da aka gudanar da kuriar jin ra’ayin jama’a a wanan babar kasa da aka baiyana da cewar ita ce ta fi yawan alumar musulmi a duniya baki daya.

Kimanin mutane miliyan 151 aka baiyana da cewar sun chanci zabe a kasar Indonesia,yayin kuma da aka baiyana cewar kashi 80 daga cikin dari na alumar kasar suka fito tashoshin zabe domin kada kuriun su a zaben shugaban kasar da aka gudanar zagaye na biyu yau litinin a kasar Indonesia.

Da dama daga cikin masu sharhi kann alamuran yau da kulum sun yi nuni da cewar bai chancanta Yudahayono ya rike ragamar mulkin kasar Indonesia ba,saboda ba zai iya magance matsalolin da kasar ke fuskanta ba a halin yanzu.

Duk kuwa da hasahen da wasu ke yi cewar Yudhayono ba zai iya jan ragamar mulkin Indonesia ba,to amman kuma bisa ga dukanin alamu yana kann hanyar lashe shugabancin kasar.

Yudhayono ya shaidawa gidan talbijin din Indonesia na SCTV cewar da yardar Allah shine zai lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar zagaye na biyu a kasar ta Indonesia yau litinin.

An dai gudanar da zaben shugaban kasar ta Indoneia na yau cikin fargaba,saboda ana tsoran cewar mai yiwa ne kungiyoyin tsagerun musulmin kasar dake da alaka da kungiyar al-Qaeda da aka zarga da laifukan hare haren boma boman da suka faru a kasar ta Indonesia ciki kuwa har da harin bomb din da ya afku a tsibirin Bali.

Duk kuwa da saurin da ake yi na kirga kuriu a zaben shugaban kasar da aka gudanar na yau,sai nan da biyar watan gobe ake sa ran hukumar zaben Indonesia zata bada sanarwar sakamakon zabe na karshe kuma a rantasr da sabon shugaban kasa a ranar 20 ga watan Octoba mai zuwa.