1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZABE A KASAR IRAQI

Yahaya AhmedJanuary 25, 2005

Zaben Iraqi, zai kasance wani al'amari mai kasadar gaske. Tuni dai `yan ta kifen kasar sun yi barazanar kai hare-hare a kan rumfuna da kafofin zaben. Daukan matakan tsaron da suka dace ne kawa abin da zai iya kare shirye-shiyen zaben daga wargajewa.

https://p.dw.com/p/BvdV
Ana iya ganin irin wadannan hotunan zabe a manyan biranen Iraqi
Ana iya ganin irin wadannan hotunan zabe a manyan biranen IraqiHoto: AP

Zaben da za a gudanar a kasar Iraqi a ran 30 ga wannan watan, shi ne farko irinsa tun da kasar ta sami `yanci kanta a shekarar 1921. Babu shakka, wannan zaben dai na dauke da kasada. Ga shi kungiyoyi `yan ta kife daban-daban na barazanar iza wuta wajen kai hare-hare a ranar zaben. Idan dai masu shirya zaben na son ya sami karbuwa, to kamata ya yi, duk bangarori da kabilun kasar su sami damar ka da kuri’unsu. Ta hakan ne kuma kadai za a iya kusantar gurin da Amirka ta sanya a gaba; wato na fara wani sabon sauyi a yankin na Gabas Ta Tsakiya gaba daya.

A kashin gaskiya dai, samun nasara wajen gudanad da wannan zaben, zai yada wani angizon sauyi a sauran kasashen Larabawa masu makwabtaka da Iraqin, inda mahunkuntan wadannan kasashen ke fargabar barkewar wani juyin juya hali, da kiran da al’ummansu za su yi na samun damar tafiyad da dimukradiyya.

Masharhanta da dama, kamar Khaula Saleh, ta sashen Larabci na nan gidan rediyon Deutsche Welle na da ra’ayin cewa, kaddamad da ranar wannan zaben, duk da barazanar ta’addanci da ake yi, wani abu ne mai ma’ana. Saboda a nata ganin, daga zaben har zuwa wata rana kuma can gaba, wato zai jinkirta samad da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Iraqin. Kazalika kuma, yin hakan zai kara karfafa wa `yan ta’addan gwiwa, wadanda ba sa sha’awar ganin kasar ta rungumi tafarkin dimukradiyya.

Babu dai wanda ya san manufofin kungiyoyin `yan ta’addan a halin yanzu a kasar ta Iraqi. Bini-bini kuma ana ta kara samun kungiyoyi da ke ta bullowa masu saunaye daban-daban. Wannan dai wani mataki ne da kungiyoyin ke dauka na bad da kammaninsu, don su yi wuyar ganuwa ga jami’an tsaro. A nan kuwa, samun ci gaba a tattaunawar tsagaita bude wuta a yankunan Falasdinawa da ake yi, zai iya taimakawa wajen kwantad da kurar rikici a Iraqin.

Sai dai kamata ya yi a tinkari wannan lamarin da hankali. Babu dai wanda zai iya karfafa cewa, gudanad da zabe a Iraqin kawai, shi ne zai samad da zaman lafiya a kasar. Za a bukaci lokaci mai tsawo kafin a iya cim ma wani sakamako, musamman a wannan kasar, inda jami’an siyasan ba su da wata goguwa da tafarkin dimukradiyya, ta yadda za su iya hada kawunan bangarori daban-daban masu bambance-bambancen kabilanci da addini.

Kazalika kuma za a dauki lokaci mai tsawo kafin a iya sake gina Iraqi. Amma duk da haka, bai kamata a fid da tsammani ba. Akwai `yan kasar da dama da ke zaman gudun hijira a ketare, tun lokacin tsohon shugaba Saddam Hussein, wanda suke zargi da gudanad da mulkin kama karya. Duk wadnnan na neman lokacin da ya dace ne don su sake komawa kasarsu ta asali. Ai kuwa zai kasance abin sha’awa, idan `yan gudun hijiran Iraqin, wadanda a galibi suka yi zama a Turai, su ka ga kuma yadda ake tafiyad da Dimukradiyya, suka ja damara, suka ba da tasu gudummuwa wajen mai da kasarsu ta asali, kasa mai bin wannan tafarkin ta dimukradiyya.