1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a Nigeria

April 20, 2007
https://p.dw.com/p/Btvj
General Buhari mai Ritaya
General Buhari mai RitayaHoto: AP

Gabannin zaben shugaban kasa dana yan majalisar tarayya a Nigeria,manazarta da alummomin kasar na ganin cewa babu alamun gudanar da zaben cikin adalci,wanda ya jagoranci korafe korafe daga bangarorin jammiyyun adawa na sanar da kauracewa zaben idan har baa dage shi ba.

Kusan dukkan jammiyyun siyasa dake tarayyar ta Nigerian dai sunyi alkawura wa alummomin wannan kasa na kawo sauyi ,bisa laakari da halin da kasar take ciki a yanzu,wadanda suka hadar da samar da dorarren wutan lantarki,da ruwan sha mai tsafta,da samrwa yara ilimi kyauta da karin guraben ayyuka.

Fitattun yan takara guda uku dake neman kujerar shugaban cin kasar dai sun hadar da dan takararr jammiyyar dake mulki ta PDP Umaru Musa Yar Adua,da Gene Mohammadu Buhari mai ritaya akarkashin tutar jamiyyar ANPP,da kuma mataimakin shugaban kasa Atiku Abukar wanda ke takara a karkashin tutar jassmmiyar AC.Dukkannin wadannan yan takara dai musulmi ne daga yankin arewacin tarayyar ta Nigeria,kana sauran kananan jammiyun kasar suma sun gabatar da tasu yan takarar.To sai dai daga cikin wadannan yan takara kowa yana da nashi hali da zaa iya banbanta shi daga sauran,kamar yadda manazarci kan lamuran siyasa a Nigeria Bawa Hassan Gusau ya bayyana

“Zaa iya bayyana dan takara akarkashin tutar jammiyyar ANNP,da kasancewa mutum ne mai hazaka,wanda keda daa bisa ga horo daya samu na harkokin tsaro ,kuma babu alamun zaiyi wasa da amanar da zaa bashi na rikon kasa a matsayin shuga,sabanin sauran yan takaran guda biyu na jamiiyyun PDP da kuma Ac,wadanda ke zama kamar ressa ne na jammiyyar dake mulki a halin yanzu.Dan takarar ANPP din ne kadai mutumin da ake ganin zai iya kawo sauyin da ake muradi”.

General Buhari dai yayi kaurin suna alokacin daya riki mulkin kasar a karkashin soji a shekarun 1980s.Ya kawo daa tsakanin alummomin wannan kasa ,musamman wajen yaki da harkoki na rashawa,batu da a halin yanzu yan Nigerian ke alfahari dashi.

Shi kuwa Umaru Musa Yar Adua na jammiyyar PDP dake zama gwamnan jihar katsina,ya taka rawa wajen yakar rashawa a jiharsa,sai dai dayawa daga cikin yan Nigeria na masa kalon dan koren shugaba Obasanjo ne,mutumin da bayan tsawon shekaru 8 yana mulkin kasar alummomi na cigaba da fuskantar karancin watan lantarki,da ruwan sha ,da man petur ,ayayinda harkokin rashawa suka mamaye koina.

Shi kuwa mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jamiiyyar AC Atiku Abubakar,mafi yawa daga yan Nigeria na ganin cewa bayace zata sake haihuwa,tunda da Obasanjo aka sanshi kafin baraka ta barke,wadda takaisu gaban kuliya.To sai dai kotuna a nigerian sun taka rawa adangane da bawa Atikun daman tsawa takara bayan an dakatar dashi.Olisa Agbakoba shine shugaban kungiyar lauyoyi na Nigeria,kuma daya daga cikin masu fafutukan kare hakkin jamaa

“Kotuna sun taka rawa wajen sanya tsanaki cikin wadannan rigingimu ,domin sun taimaka wajen wanke irin miyagun ababanda yan siyasa suka aiwatar,don haka dolemu yaba musu wajen warware wadannan matsaloli”.

To abangaren kungiyoyin jama sun koka dangane da rashin basu dana sanin halin da ake ciki dangane da shirye shiryen zaben,musamman aq bangaren hukumar zaben.Chukwuemeka Eze shine shugaban hadaddiyar kungiyar tabbar da zaman lafiya na kasashen yammacin Afrika aLagos

“Sunyi tambayoyi da dama wadanda baa basu amsarsu ba,abunda kullum muke ji shine,a shirye muke ,kuma wannan zabe zai gudana cikin gaskiya da adalci.To bawai abunda kuke ikirarin aiwatarwa bane,amma harda yadda mu muke gani adangane da ku”