1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe mai sarkakiya a Afirka ta Tsakiya

Zainab Mohammed AbubakarDecember 26, 2015

A ranar Laraba ne Janhuriyar Afirka ta Tsakiya ke gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, a wani mataki warware rikicin addini da kasar ta tsinci kanta a ciki.

https://p.dw.com/p/1HU2g
Zentralafrika Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Zaben shugaban kasar da 'yan majalisar dokokin da ya sha jinkiri dai, ya biyo bayan kuri'ar jin ra'ayin jama'a ne kan sabon kundin tsarin mulkinta ne, da ya gudana ranar 13 ga watan Disamba, kundin da ya samu amincewa da kashi 93 daga cikin 100 na yawan masu zaben. Hakan dai ya nunar da yadda mafi yawan 'yan Afirka ta Tsakiyar ke hankoran komawa rayuwarsu ta yau da kullum kamar yadda suka saba a baya. A cewar fraiministan kasar Mahamat Kamooun dage zaben ya zamanto wajibi.

Ya ce" Muna muradin gudanar da ingantaccen zabe kuma cikin nasara, tare da tabbatar da adalci bisa tafarkin demokradiyya".

Bayan kazamin dauki ba dadi tsakanin mabiya manyan addinan kasar biyu daya dauki tsawon shekaru biyu yana gudana, rikicin da ya tilasta kashi 10 daga cikin 100 na al'ummar kasar tserewa domin neman mafaka a ketare, jama'a na fatan ganin cewar an kawo karshen wannan zubar da jini a wannan kasa da Allah ya hore wa dumbin albarkatun kasa. Sai dai wasu 'yan kasar na ganin cewar 'yan takara 30 da ke neman gujerar shugabancin kasar, sun yi yawa.

Zentralafrikanische Republik - Anicet Clément Guiyama Massogo
Dan takara Anicet Clément Guiyama MassogoHoto: DW/J. M. Barès

"Da zarar aka sanarwa mutane cewa 'yan takara 30 ne gare mu abun ma na bada dariya domin karamar kasa kamar wannan tamu da ke cikin mawuyacin hali na da yawan 'yan takara haka, ni sai ince abun ya yi yawa kwarai, kuma hakan ya nunar da cewa 'yan siyasar kasar nan kowa ta kan shi ya ke ba wai don son kasar ba."

Duk da kasancewar sojojin MDD dana Faransa dubu 11 a Afirka ta tsakiyar dai, har yanzu mafi yawa daga cikin yankunan kasar na hannun shugabannin tawaye ko kuma mayakan sakai.

A cewar fraiministan Afirka ta Tsakiyar Mahamat Kamooun dai, dage zaben na da nasaba da kura kurai da aka fuskanta a bangaren ma'aikatan gudanar da zaben.

Ya ce" Mun lura da cewar alokacin da aka kada kuri'ar jin ra'ayin dangane da sabon kundin tsarin mulkin kasar, ma'aikatan kula da zaben basu da masaniya dangane da yadda aikin yake, wanda ya kai su rubuta bayanai da ba daidai ba,hakan ne yasa muka soke wasu kuri'un. Ko shakka babu muna bukatarshirya horarwa, tare da samo mutanen da suka dace , ganin cewar wannan zaben yana da matukar muhimmanci fiye da na jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya".

Zentralafrikanische Republik Wahlkampf - Anhänger Patrice-Edouard Ngaïssona
Yakin Neman zaben Patrice-Edouard NgaïssonaHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Janhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fara afkawa cikin wadi na tsaka mai wuya ne dai a watan Disamba shekara ta 1965, shekaru biyar bayan samun 'yancin kasar, lokacin da Jean -Bedel-Bokassa ya hambarar da mulkin shugaba David Dacko. Bokassa ya dare karagar shugabanci a watan Janairu 1966, tare da nada kanshi a matsayin shugaban mulkin mulkiyya a shekarata 1977 a wani buki na almubazzaranci da ya ja hankalin duniya. Daganan ne kuma kasar ta cigaba da fuskantar rigingimu daban daban kama daga na siyasa da kabilanci zuwa na addini da ya hambarar da shugaba na karshe Francois Bozize a watan Maris 2013.