1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe shugaban kasa a jamhuriyar Benin

March 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4m

A ranar Lahadin nan ne idan Allah ya kai mu zaá gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a jamuriyar Benin. Bayan gaza samun adadin kuriún da ake bukata a zagayen farko na zaben wanda aka gudanar makwanni biyu da suka gabata, hukumar zaben ta ce zaá sake karawa tsakanin Yayi Boni masanin harkokin tattalin arziki wanda ya taba rike Bankin raya kasa na yammacin Afrika da kuma Adrien Houngbedji tsohon P/M kasar. Shugaban hukumar zaben Sylvain Nouatin yace Kotun tsarin mulkin ta kasar ta bukaci jinkirta zaben ya zuwa nan da yan kwanaki domin bada ta yin cikkaken shiri, to amma shugaban kasar mai barin gado Mathieu Kerekou ya umarci kotun ta bari a gudanar da zaben a ranar Lahadi. Tsarin mulkin kasar ya tanadi gudanar da zagaye na biyu na zaben cikin kwanaki goma sha biyar, bayan zaben farko da aka kada. A sakamakon da aka baiyana a zagayen farko na zaben, Boni ya sami kashi 36 cikin dari na kuriún yayin da abokin hamaiyar sa Houngbedji ya sami kashi 24 cikin dari na adadin kuriun da aka kada.