1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Afurka ta Kudu

April 16, 2004

Alkaluma sun nuna cewar jam'iyyar ANC ta lashe kusan kashi 70% na kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar a Afurka ta Kudu ranar laraba da ta wuce

https://p.dw.com/p/Bvkb
Kimanin mutane miliyan 20 suka yi amfani da hakkinsu domin kada kuri'a a zaben ATK
Kimanin mutane miliyan 20 suka yi amfani da hakkinsu domin kada kuri'a a zaben ATKHoto: AP

A hakika dai babu wani da yayi tababa a game da nasarar ANC a zaben da aka gudanar a ATK a wannan makon da kuma cewar a mako mai zuwa majalisar dokokin kasar zata sake tabbatar da shugaba Thabo Mbeki akan karagarsa ta mulki. Abu daya da aka rika tababa game da shi shi ne ko Ya-Allah za a samu wani canji na rinjayen kashi biyu bisa uku da ANC ke da shi a majalisar dokoki. Ala-ayyi-halin dai jam’iyyar ta samu cikakken goyan baya domin jan akalar mulkin ATK har tsawon shekaru biyar masu zuwa. Wani abin lura a nan kuwa shi ne kasancewar hukumar zabe ta kasar ta shirya zaben akan wata kyakkyawar sibga ta adalci, bisa sabanin yadda aka saba gani a wasu kasashen Afurka dake ikirarin bin mulki na demokradiyya, amma suke caba magudi a lokutan zabe. Al’umar ATK dake da ikon kada kuri’a sun yi amfani da wannan dama domin mara wa mutanen da suka taka rawar gani wajen ‚yantar da su daga kangin bauta na mulkin wariya da banbancin launin fata suka kuma taimaka gwargwadon ikonsu domin daga matsayin rayuwar bakar fata ‚yan rabbana ka wadata mu a kasar. Ko shakka babu za a yi wasu shekaru da dama nan gaba jam’iyyar ANC tana mai jan akalar siyasar ATK, duk kuwa da cewar har yau ba ta cimma bukatunta na samar da wadata ga kowa-da-kowa ba. Amma muhimmi abu shi ne kasancewar al’umar ATK sun nakalci ma’anar demokradiyya a cikin shekaru 10 da suka wuce suna masu fatali da ire-iren matakan nan na tashe-tashen hankulan siyasa da aka sha fama dasu a daidai lokacin da kasar take kan hanyarta ta canjin alkibla. Wannan muhimmin ci gaba ne dake ba da kwarin guiwa a game da makomar kasar. Wani abin da zai taimaka kuma shi ne a ci gaba da nakaltar manufofin demokradiyya ta yadda ba za a wayi gari ATK ta koma karkashin wani tsarin mai kama da mulkin jam’iyyar siyasa daya kwal ba dangane da kakkarfan angizon da ANC ke da shi yanzu haka. Ita kuma ANC a nata bangaren tana da jan aiki gabanta. Wajibi ne ta bi wata hanya madaidaiciya domin aiwatar da garambawul da sake rabon filaye tsakanin al’umar kasar. Kazalika wajibi ne ta sake yunkura wajen yaki da cutar nan ta Aids dake dada yaduwa tsakanin jama’a ta kuma tinkari matsalar rashin aikin yi da tuni ta zama ruwan dare, musamman tsakanin matasa bakar fata da ake yayesu daga manyan makarantu na kasar ATK. A lokacin da yake jawabi ga jama’a, bayan da alkaluma suka ba wa jam’iyyarsa ta ANC kimanin kashi 69 da rara cikin dari na jumullar kuri’un da aka kirga daga kashi 95% na illahirin mazabun ATK shugaba Thabo Mbeki ya jaddada cewar ANC zata ci gaba akan manufofinta na canji kuma ba zata yarda, murna ta koma ciki ga miliyoyin talakawan ATK bakar fata da suka saka dogon buri akanta a game da kyautata makomar rayuwarsu ba. Shugaban na ATK yayi alkawarin samar da guraben aikin yi ga jama’a da kuma daukar nagartattun matakan yaki da cutar Aids dake dada yaduwa tsakanin bakar fatar kasar.