1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali

Gazali Abdou TasawaFebruary 21, 2016

Duk da yake zaben ya gudana a cikin wani yanayin na kin yarda da juna tsakanin masu mulki da 'yan adawa, amma rahotanni daga kasar ta Nijar na cewa zaben ya gudana a cikin kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/1HzRo
Niger Wahl Wähler in Niamey
Hoto: DW/A. Amadou

A jamhuriyar Nijar jama'a an kammala kada kuri'arsu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da kasar da ya gudana wannan Lahadi. Ko da yake zaben ya wakana ne a cikin wani yanayi na kin yarda da juna tsakanin masu mulki da 'yan adawar kasar wadanda suka yi korafin yiwuwar tafka magudi a zaben, kawo yanzu dai rahotanni daga kasar ta Nijar na cewa zaben ya gudana a cikin kwanciyar hankali a ilahirin yankunan kasar.

Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an samu dan jinkiri wajen bude rumfunan zabe a wasu unguwannin birnin Yamai da ma a wasu yankuna na kasar. Batun da madugun 'yan adawar Nijar Alhaji Seini Oumarou ya yi korafi a kansa kamar yadda ya shaida wa wakilinmu na birnin Yamai Mahaman Kanta jim kadan bayan kada kuri'a.

Sai dai duk da haka wakilanmu sun ruwaito cewa a ko ina jama'a sun fito dafifi domin kada kuri'ar tasu.

Niger Wahl Wählerin in Niamey
Tantance masu kada kuri'a a birnin YamaiHoto: DW/M. Kanta

'Yan Nijar kimanin miliyan bakwai da rabi ne ake sa rai za su kada kuri'ar tasu domin zaben sabon shugaban kasa daga cikin 'yan takara 15 da suka hada da shugaba mai ci Alhaji Mahamadou Issoufou wanda ya yi ikirarin lashe zaben tun a zagayen farko da Alhaji Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD Nasara wanda shi kuma ya yi ikirarin yin waje da shugaban mai ci tun a zagayen farko da kuma Hama Amadou shugaban jam'iyyar Lumana Afirka da yanzu haka ke tsare a gidan kurkuku na garin Filingue a bisa zargin da hukumomi ke yi masa na kasancewa da hannu a cikin wata badakalar cinikin jarirrai.