1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamna a jihar Kogi ta Najeriya

Ubale MusaNovember 20, 2015

Hankulla sun karkata kan yadda sabin hukumomin Najeriya za su shirya zaben jihar Kogi da ke zaman na farko ga shugaban kasar da ma shugaban hukumar zabe.

https://p.dw.com/p/1H9oq
Hoto: Plaucheur/AFP/Getty Images

Sama da al'ummar jihar ta Kogi miliyan guda da dubu dari daya ne dai ake saran za su fito domin kada kuri'a a zaben gwamnan jihar mai tasirin gaske. Duk da cewar dai yana daya a cikin jihohin kasar 36, kasancewarsa na farko ga shi kansa shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu. Dama shugaba Muhammad Buhari da ya hau gado a tsarin sauyi. Tuni dai hukumar zaben kasar ta INEC ta ce ta shirya tsaf da nufin ba marada kunya a zaben da wasu ke yi wa kallon dorawa a bisa nasarorin baya ko kuma komawa ya zuwa ga tsohuwar al'ada. Mr Nick Dazang dai na zaman kakaki na hukumar da kuma a cewarsa shirye shrye sun kai lungu da karkara ta jihar Kogi da nufin tabbatar da adalci a tsakanin kowa.

Wahl Nigeria Abuja
Hoto: DW/Uwaisu A. Idris

" Mun rarraba kayan zabe na sirri da kuma wanda ba na sirri ba, musamman na sirri tun a ranar Alhamis mun tura su a kananan hukumomi 21 a jihar Kogi sannan a wannan rana zamu tura sauran kayayaki zuwa ga gundumomi 239 a fadin jihar Kogi, sannan kuma da asubahi da yardar Allah jami'an mu na zabe, da kuma jami'an tsaro za su isa daga gundumomi zuwa cibiyoyi inda za'a yi zabe a ranar Asabar da safe. Don haka mun shirya sosai domin wannan zabe. "

Ga batun tsaro ma dai rundunar yan sandan kasar ta Najeriya tace ta tura yan sanda kusan 13,000 da nufin bada kariya ga 'yan zabe na jihar da ke da iyaka da akalla jihohi 10, da kuma tuni wasu jam'iyyun kasar suka fara korafin shiri na magudi. Akalla dai 'yan takara 17 ne dai ake saran za su fafata a cikin zaben da ke da tasiri ga al'ummar jihar ta Kogi dama Tarrayar Najeriya gaba daya. Ana dai kallon zaben a matsayin dama ta kasar da ko dai ta dora a bisa nasarorin baya na zaben shugaban kasar da gwamnoni na jihohi, ko kuma komawa zuwa gidan jiya da ma komawa baya ga harkar demokaradiyyar mai tasiri.

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Duk da cewar dai tuni shugaban kasar ya fito fili domin jaddada aniyyarsa ta zama dan kallo a cikin harkokin zabe, akwai dai tsoron yiwuwar wasu a cikin jam'iyyarsa ta APC na nuna karfin iko da nufin tabbatar da komawar Kogin zuwa ga tsintsiya ko ana ha maza ha mata. Abun kuma da a cewar Dr Garba Umar Kari da ke zaman masani kan harkoki na siyasa ke iya shafar yunkurin kasar na tabbatar da yancin zabe a tsakanin kowa.

" Sai an gudanar da wannan zabe ne mutane za su iya yanke hukuncin cewa ikirarin da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da kuma Farfesa Mahamudu Yakubu shugaban hukumar zabe da ma masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe suka jibanci sha'anin na zabe ya zo daidai ko ba daidai ba. To amma dai ni ma ina ganin bisa saninsa da muka yi Shugaba Buhari ba zai sa hannu cikin harkokin zabe ba to amma kasancewar shi daya ne kuma jam'iyyarsa ta sha alwashin cewa sai ta kwato wannan jiha, kenan ko shi bai yi ba ba mamaki wasu mukarrabansa bisa rashin saninsa su za su yi."

abun jira a gani dai, na zaman sakamakon da ke shirin fita daga zaben dama karbuwarsa tsakanin daukcin masu ruwa da tsaki da batun zabe a jihar.