1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU, Italiya, Renzi, Jamus

Abdul-raheem Hassan
December 5, 2016

Sakamakon zaben raba gardama na kasar Italiya ya jefa kasashen Turai cikin rashin tabbas, bayan da yan kasar suka kada kuri'ar kin amincewa da bukatar Firaministan na yin kwaskwarima ga tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/2Tl8D
Italien | Ministerpräsident Matteo Renzi kündigt nach gescheitertem Referendum seinen Rücktritt an
Firaministan Italiya Matteo RenziHoto: REUTERS/A. Bianchi

 

Sakamakon zaben raba gardamar bai yiwa Firaministan Italiya Matteo Renzi dadi ba, wanda ya yi alkawarin cewa zai yi murabus idan 'yan kasar suka ki yi watsi da bukatar da ya gabatar ta yin gyara ga kundin mulkin kasar:

Italien | Ministerpräsident Matteo Renzi kündigt nach gescheitertem Referendum seinen Rücktritt an
Firaministan Italiya Matteo RenziHoto: Reuters/T. Gentile

"Na so na rage yawan 'yan majalisun dokoki ciki har da majalisar dattijai da kuma matakan gwamnati a gundumomi. To amma ban yi nasara hakan ba. Ina godiya ga abokan aiki na da gundumawar da suka bayar zan kuma mika takarda ta ta murabus ga shugaban kasa."

Firaministan Matteo Renzi ya yi ganawar sirri da shugaban kasar Sergio Matterella yaban sakamakon zaben, tuni dai matakin ya jefa daukacin kasashen Turai masu amfani da kudin bai daya na Euro cikin rudani da rashin tabbas inda aka wayi gari harkokin kudade da kasuwannin hannun jari a kudancin Asia suka fara tangal tangal. Ko da yake daga baya darajar kudin na Euro ya farfado daga baya.

Kasancewar Italiya kasa ta uku mafi karfin tattalin arziki a turai ya sanya fargaba ta yiwuwar samun matsalar koma bayan tattalin arziki nahiyar Turan. Sai dai Jamus kasa mafi karfin tattalin arziki a turan da take mayar da martani ga wannan yanayi da aka shiga a Italiya, ta bukaci kwantar da hankula tana mai cewa babu wani dalili na fadawa matsalar rikicin kudin Euro. Wolfgang Schäuble shi ne ministan kudi na Jamus:

Deutschland Auftakt der deutschen G20-Präsidentschaft 2017
Wolfgang Schäuble, ministan kudi na Jamus.Hoto: picture alliance/dpa/B. von Jutrczenka

"Ko kadan batun tattaunawa kan matsalar rikicin kudin Euro bai ma taso ba, babu wani wata hujja ta yin hakan."

Shi ma da yake tsokaci shugaban rukunin kasashe 19 masu amfani da kudin bai daya na Euro Jeroen Dijsselbloem wanda kuma har ila yau shine ministan kudi na kasar Netherland ya sassauta damuwa kan yiwuwar samun matsalar rikicin kudin euro a dalilin sakakon raba gardamar na Italiya.

Luxemburg Treffen der Finanzminister
Jeroen Dijsselbloem, shugaban rukunin kasashe masu amfani da kudin Euro Hoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

Ya shaidawa yan jarida a Brussels cibiyar tarayyar turan cewa babu wani abu da zai sauya ta fuskar tattalin arziki. 

"Yace wannan sakamako ne na tafarkin dimokradiyya akan abu guda, ba zai sauya komai ba ta harkar tattalin arziki ko sha'anin Bankuna."

Duk da wannan tabbaci dai har yanzu ana nuna shakku akan ko kasar za ta iya tunkarar kalubalen da sakamkon zaben hai haifar.