1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben jihohin Jamus Guda Uku

March 27, 2006

A jiya lahadi aka gudanar da zabe na farko a jihohin Jamus guda uku tun bayan kafa babbar gwamnatin hadin guiwa a Berlin

https://p.dw.com/p/Bu10
Gwamnonin jihohi uku na Jamus
Gwamnonin jihohi uku na JamusHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Kamar dai yadda aka saba bisa al’ada, zabubbukan jihohin Jamus sun zama tamkar wani mizani ne da ake amfani da shi wajen bayyana irin goyan baya da gwamnatin tarayya ke da shi tsakanin jama’a. A sakamakon haka aka dokata wajen sauraron sakamakon zabubbukan jihohin kasar guda uku da aka gudanar a jiya lahadi, wadanda su ne na farko tun bayan kafa mulkin hadin guiwa tsakanin Christian Union da Social democrats. Kuma ko da yake jam’iyyar Social Democrats ta samu koma bayan kuri’u a jihar Baden-Württemberg sannan ita kuma Christian Democratic Union tayi asarar kuri’u a jihar Rhinland-Palatinate, amma sakamakon zabubbukan gaba daya ya zama mai ba da cikakken goyan baya ne ga gwamnatin hadin guiwa na bangarorin guda biyu dake ci a fadar mulki ta Berlin. Jam’iyyar da sakamakon zaben bai zo mata da dadin ba ita ce ta ‘yan Free Democrats, wadda kafin wannan zabe take da hannu a gwamnatocin dukkan jihohin guda uku, amma a jiya aka yi awon gaba da ita a jihohin Sachsen-Anhalt da Rhinland-Palatinate. Wannan kuma babban koma baya ne ga angizonta na siyasa. Domin kuwa a yanzun gwamnatin hadin guiwar dake mulki ba ta bukatar goyan baya daga wannan jam’iyya a wajen cimma rinjayen kashi biyu bisa uku a majalisar gwamnonin jiha domin wanzar da tsarin dokoki. Ko da yake a demokradiyyance mutum zai iya dari-dari da wannan ci gaba da ake samu, amma a daya bangaren zai zama tamkar matsin kaimi ne ga gwamnatin hadin guiwar domin ta tashi tsaye wajen tafiyar da manufofinta na garambawul. Ita kuma shugabar gwamnati Angela Merkel wajibi ne a yanzu ta kara mayar da hankalinta ga manufofi na cikin gida. Sakamakon tattaunawar da gwamnatin hadin guiwar zata yi a game da shawarar garambawul ga al’amuran kiwon lafiya shi ne zai zama zakarar gwaji a game da irin alkiblar da gwamnatin zata fuskanta bayan zabubbukan jihohin guda uku. Nan gaba dai za a gudanar da wasu zabubbukan kuma hankali zai sake karkata ne zuwa Berlin domin bitar salon kamun ludayin gwamnatin.