1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kananan hukumomi a Saudiyya

February 10, 2005

A yau alhamis ne aka gabatar da matakin farko na zaben kananan hukumomi a Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya

https://p.dw.com/p/BvdE
Masu zabe a Saudiyya
Masu zabe a SaudiyyaHoto: AP

An saurara daga Sultan Bin Halal, kwararren masani akan al’amuran na’ura mai kwakwalwa, wanda kuma ke daya daga cikin ‚yan takarar zaben kananan hukumomin a birnin Riyadh yana mai bayanin cewar muhimmin abin da yake fatan cimma idan ya samu nasarar shiga majalisar karamar hukumar shi ne taimaka wa matasa, wadanda ke bukatar wuraren nishadi a birnin na Riyadh, a maimakon gidajen gahawa da su kan yi cincirindo a cikinsu. Da yawa daga wadannan matasa ba su da tayi illa su rika kai da komo a mota ko watangaririya a tituna suna masu gundura da rayuwarsu. A saboda haka suke bukatar wuraren nishadi da suka hada da wasannin motsa jiki, a cewar Sultan Bin Halal, wanda ‚yan uwansa dake taimaka masa a yakin neman zabe suka sikankance cewar zai cimma nasara akan abokin takararsa, wanda ke tallata kansa a jaridu ya kuma haya wani kasaitaccen gini, inda yake gayyatar mutane zuwa liyafar cin abinci da sauraren wake na adabi da hikayoyi da shauransu. Wasu daga cikin ‚yan takarar dai sun kashe makudan kudi a yake-yakensu na neman zabe, musamman ma dillalan plot-plot, saboda imanin da suka yi na cewar kasuwarsu zata dada bunkasa idan har sun samu kafar shiga majalisar gunduma. Amma a daura da haka da yawa daga jama’a sun ki su yi rajistar zaben a saboda ainifin wannan dalilin. Da yawa daga cikinsu sun yi imanin cewar ‚yan takarar kawai cika baki suke wajen gabatar da alkawururrukan da ba zasu iya cikawa ba. Amma bisa ga ra’ayin Muhammed Al Ghamdi, babban editan jaridar Gazzet ta saudiyya, wannan zaben tamkar zakaran gwajin dafi ne a game da sabuwar alkiblar siyasar da kasar ta Saudiyya ta fuskanta. Ya ce wannan zaben shi ne matakin farko akan hanyar gabatar da tsarin mulkin demokradiyya a kasar Saudiyya. Bai dai bayyana damuwarsa a game da gaskiyar cewa tsarin mulkin demokradiyyar an gabatar da shi ne daga sama, amma ba abu ne da ya zo daga tushe ba. Al Ghamdi ya ce tilas ne a tafi sannu a hankali saboda al’umar Saudiyya mutane ne dake da ra’ay na mazan-jiya. Kuma ko da yake a wannan karon ba a ba wa mata damar shiga zaben ba, ba shakka a zabe na gaba zasu samu irin wannan dama a cewar babban editan jaridar ta Gazzett, ya kuma kara da cewar:

Bisa ga dukkan alamu mata zasu shiga a dama da su a zaben kananan hukumomi na gaba. An samu bayani daga Yerima Saud al-Turki cewar za a ba wa mata damar shiga zaben majalisun gundumomi, kuma su kansu matan sun bayyana cewar nan gaba zasu tsaya takarar zabe.