1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Kasar Afghanistan

October 11, 2004

Zaben farko da aka gudanar a demokradiyyance a kasar Afghanistan ya tafi salin alin ba tare da hargitsi ba

https://p.dw.com/p/Bvfk
Zaben Afghanistan
Zaben AfghanistanHoto: AP

Abin mamaki da al’ajabi a game da zaben na kasar Afghanistan shi ne yadda ya tafi salin alin ba tare da tashe-tashen hankula ba, duk kuwa da cewar wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan zabe na demokradiyya a kasar wacce ta sha fama da yake-yake na basasa da danyyen mulki na kama karya. Abu daya da ya so ya kawo cikas ga wannan kyakkyawan yanayi na zabe inda dubban daruruwan al’umar Afghanistan suka yi cincirindo domin kada kuri’unsu shi ne tangarda da aka samu dangane da tawadar da aka rika amfani da ita domin yi wa masu zaben lambar shaidar ta yadda ba zasu samu damar kada kuri’a fiye da sau daya kamar yadda aka kayyade ba, wacce daga bisani aka gano cewar bata da tasiri saboda ana iya goge ta nan take. Wannan tabargazar ta kusa ta sanya murna ta koma ciki. Saboda ‚yan takara 15 daga cikin ‚yan takarar neman kujerar shugabancin Afghanistan suka yi kiran dakatar da zaben, domin a ganinsu babu adalci a cikinsa, kuma suka ce faufau ba zasu yarda da sakamakonsa ba. Amma duk da haka, abin lura shi ne ganin yadda al'amar Afghanistan suka dokata wajen shiga wannan zabe, inda tun da sanyin safiyar asabar suka fara cincirindo a kofar rumfunan zaben, musamman ma a Kabul fadar mulkin wannan kasa. Zaben kasa wani babban kalubale ne ta la’akari da cewar kimanin kashi 50% na maza da kuma 80% na mata a Afghanistan ba su iya rubutu da karatu ba kuma da wuya ake iya kutsawa wasu larduna ko yankunan karkararta. Hakan ya sanya ba zata yiwu a shimfida ka’idojin zaben da aka saba aiwatarwa a kasashen yammaci domin zama mizanin zaben na Afghanistan ba. Su kansu matsalolin da aka fuskanta a zaben abubuwa ne da aka saba gani a zabubbuka na kasashen yammaci kuma ana iya yin gyara wajen shirya zabe na gaba. Amma duk wata magana ta soke sakamakon zaben a daidai wannan lokacin da muke ciki yanzun, ba abin da zata tsinana illa ta sanya murnar al’umar Afghanistan ta koma ciki su kuma dawo daga rakiyar duk wata manufa ta demokradiyya. Masu iya magana dai su kan ce wai: Da babu gwamma ba dadi. Abu mafi alheri shi ne a dauki nagartattun matakai domin kauce wa ire-iren wannan tabargaza a zabubbuka na gaba.