1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Brazil

October 2, 2006

A zaben jiya lahadi shugaba Lula bai cimma gagarumin rinjaye ba kuma a saboda haka tilas a koma zagaye na biyu ga zaben shugaban kasar Brazil

https://p.dw.com/p/Btxx
Shugaba Lula da Silva na Brazil
Shugaba Lula da Silva na BrazilHoto: AP

Idan mutum ya waywayi baya a cikin shekaru hudun da suka wuce tilas yayi mamaki akan goyan bayan da kusan kimanin kashi 50% na al’umar Brazil suka ba wa shugaba Lula da Silva, musamman ma ta la’akari da tabargaza iri-iri da aka sha fuskanta tsawon wa’adin mulkinsa. Jam’iyyarsa ta ma’aikata wato PT ta yi amfani da kudade na haram domin tallafa wa yakinta na neman zabe tare da ba wa wasu wakilan majalisar dokoki toshiyar baki. Kusan dukkan shuagabannin jam’iyyar suka yi murabus sakamakon wannan tabargaza. Amma ga alamu akwai wasu dalilai guda uku da suka sanya al’umar brazil suka sake zaben shugaba Lula da Silva. Da farko dai shi ne kasancewar kimanin kashi biyu bisa uku na al’umar Brazil sun hakikance cewar dukkan jami’an siyasar kasar jirgi daya ne ke dauke da su dangane da tabargazar cin hanci da almundahana, kamar yadda sakamakon wani binciken ra’ayin jama’a ya nunar. Da yawa daga al’umar kasar sun hakura da wannan kaddara ta cin hanci dake addabar kasarsu duk da ci gaban da aka samu a ‘yan shekarun baya-bayan nan. Kuma wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya suka zabi mutane kamarsu Fernando Coller de Mello da Paulo Maluf da Joaquim Roriz, wadanda su ne shuagabannin cin hanci a kasar ta Brazil. Kazalika wannan rungumar kaddara da jama’a suka yi shi ya sanya suka yi ko oho da kiraye-kirayen da abokin takarar Lula da Silva, Geraldo Alckmin ya rika yi a yakinsa na neman zabe. Bugu da kari ma ita kanta jam’iyyar Soacil Democrats PSDB ta Geraldo Alckmin akwai kurar cin hanci da tabargaza iri daban-daban tattare da ita a karkashin mulkin Henrique Cardoso, a yayinda abokiyar hadin guiwarta PFL mai ra’ayin mazan jiya take mulki na nuna son kai tsawon shekara da shekaru a jihar Bahia. Dalili na biyu a game da nasarar Lula da Silva kuma shi ne nagartattun maufofin tattalin arzikin da gwamnatinsa ke bi. Gwamnatin ta ci gaba da kayyade gibin kasafin kudinta tare da biyan basusukan dake kanta da dakatar da hauhawar farashin kaya. Dalili na uku kuwa shi ne manufofin gwamnatinsa na kyautata jin dadin rayuwar talakawa, inda da yawa daga cikin talakawan kasar suka rika samun taimako na gwamnati a karo na farko a rayuwarsu. Hakan ya taimaka aka rage gibin dake akwai tsakanin rukunoni daban-daban na kasar Brazil da kuma sassauta radadin talaucin dake addabar ‘yan rabbana ka wadata mu a kasar. Bisa ga dukkan alamu dai Lula da Silva ya kasa cimma gagarumin rinjaye ne, duk da cikakken goyan bayan da ya samu daga talakawan kasa ‘yan rabbana ka wadata mu, saboda kin halartar wani zaman mahawara da aka shirya yi ta gidan telebijin kasar dab da zaben a ranar alhamis da ta wuce. A yanzu ba abin da ya rage illa a dakaci ranar 29 ga watan oktoba aga yadda al’amura zasu kaya. Rana dai bata karya sai ko uwar ‘ya tayi kunya.