1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar kongo

July 19, 2006

An shiga yakin neman zabe gadan-gadan a kasar Kongo

https://p.dw.com/p/Btz2
Yakin neman zaben Kongo
Yakin neman zaben KongoHoto: picture-alliance / dpa

A duk ko’ina ka bi a titunan birnin Kinshasa zaka tarar da alluna dauke da hutunan ‘yan takarar neman zaben shugaban kasar ta Kongo. Gaggan ‘yan takarar sun kashe miliyoyin dalar Amuka a yakinsu na neman zabe. A halin yanzu haka hotunan shugaba Joseph Kabila da babban abokin takararsa Jean-Pierre Bemba duk sun yadu a fadin kasar Kongo. Dangane da ‘yan takara masu karamin karfi kuwa su kansu ne ke zayyana allunansu na takarar zaben. Gaba daya ‘yan takarar 33 ne ke gwagwarmayar samun kujerar shugaban kasa. Babban abin da shugaban hukumar zabe Appolinaire Malu-Malu ke fata shi ne kome ya tafi salin alin kuma kasar ba zata sake fadawa cikin munanan tashe-tashen hankula bayan zaben ba.

“Wannan ba mummunan yaki ba ne ba, a’a, tserereniya ce kawai, kuma wajibi ne a samu mai nasara da mai asara. Amma masu asarar zaben duk da haka zasu ci gaba da taka muhimmiyar rawa a siyasar kasa. Muhimmin abu shi ne su girmama tsarin da ake kai.”

Wani abin lura a game da zaben na kasar Kongo dai shi ne kasancewar kusan ba abin da ya banbanta shi da yadda al’amura suka kasance a wannan kasa misalin shekaru 46 da suka wuce lokacin da kasar ta samu ‘yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na kasar Belgium. Wasu daga cikin ‘yan takarar ma suna amsa sunayen ‘yan takara ne na wancan lokaci, wato dai a takaice ‘ya’yan wadancan tsaffin jami’an siyasa ne, wadanda suka hada da Lumumba da Mobuto da Kabila. Ita ma ‘yar tsofon zababben shugaba Kasavubu zata shiga takarar zaben. Komai dai zai danganta ne da irin rawar da wadannan ‘ya’yan jami’an siyasa zasu taka dangane da sakamakon zaben ko Ya-Allah zasu amince da kuri’ar ta demokradiyya. Wani dan jarida da ake kira Ben-Clet Kankonde Dambu ya bayyana fatan samuwar hakan inda yake cewar:

“Babban abin da ya fi daukar hankalin mutane a yake-yaken da muka sha fama dasu a cikin shekaru 46 da suka wuce shi ne wane ne ke da fada a ji. An fuskanci juye-juyun mulki, inda aka wayi gari shuagabanni na tafiyar da al’amuran mulki ba tare da samun amincewa daga jama’a ba. Kuma wadannan shugabannin su ne suka kai kasar suka baro.”

Kungiyar Tarayyar Turai dai ta ba da gudummawar sojoji 1100 domin tabbatar da cewar zaben ya tafi salin alin ba tare da tashin hankali ba. Kuma a halin yanzu haka muhimmin abin da sojojin ke kokarin yi shi ne ganin cewar ba a bai wa sojojin shugaba Kabila wata dama ta cin karensu babu babbaka a lokacin zaben ba. Hakan ba shakka zai taimaka a samu nasarar zaben.