1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Kuwait

June 29, 2006

A karon farko a cikin tarihin Kuwait an ba wa mata damar tsayawa takarar zaben majalisa a kasar

https://p.dw.com/p/BtzZ
Mata a yakin zaben Kuwait
Mata a yakin zaben KuwaitHoto: AP

A hakika dai majalisun dokoki a kasashen Larabawa ba su da wani tasiri ko angzo na a zo a gani. Galibi akan fake da wadannan kafofi ne domin kwantarwa da al’umar kasashen hankalinsu da kuma bayyana wa duniya cewar kasashen na bin mulki na demokradiyya. Ita ma kasar Kuwait mai arzikin man fetur ta dade akan wannan manufa kafin ta canza alkibla ta durfafi sahihin tsari na demokradiyya tsantsa, lamarin da zai kara tabbatuwa sakamakon zaben kasa na yau alhamis, inda majalisar dokokin zata zama wata kafa mai zaman kanta a kasar ta Larabawa. Wani abin lura dai dangane da kasar Kuwait shi ne ko da yake kasar na da yawan al’uma miliyan biyu da dubu dari shida amma duka-duka mutane dubu dari uku da hamsin ne ke da ikon shiga zabe. Domin kuwa ragowar baki ne daga kasashen ketare da suka hada da Indiyawa da ‘yan Pakistan da Iran, ko da yake da yawa daga cikinsu sun dade da zama a kasar mai arzikin man fetur. A farkon watan mayun da ya gabata majalisar dokokin ta fara nuna angizonta, inda ta bayyana adawarta da nadin da aka yi wa Sheikh Saad Al-Abdullah a matsayin shugaban kasa bayan mutuwar Shaikh Jaber el-Ahmad, wadanda dukkansu tsattsan Sabah ne. Bayan kai ruwa-ranar da aka yi majalisar ta kakkabe sabon shugaban bisa dalilan da aka ce wai na rashin lafiya, amma aka maye gurbinsa da Sabad al’ahmad al-Sabah. Tun kuwa tafiya ba ta je nesa ba aka shiga takun-saka tsakaninsa da majalisar, wadda ta nemi da a rarraba kasar zuwa mazabu goma ko kuma akalla mazabu biyar, duk kuwa da cewar ita kanta majalisar ce a shekarar da ta gabata ta amince da a bai wa mata damar shiga zabe, wadanda kuma yawansu ya kama mata dubu 200 daga cikin illahirin mutane dubu 350 dake da ikon kada kuri’a a Kuwait. Kuma ko da yake har yau ba# a shawo kan wannan sabani ba, amma an rushe majalisar aka kuma sanya ranar zabe na gaba da wa’adi. Manazarta dai sun ce ba wani sauyi na a zo a gani da za a samu daga zaben na yau alhamis. ‘Yan takara 300 ne ke neman wakilci a majalisar abin da ya hada har da tsaffin wakilai 47 daga cikin wakilanta su 50. Bugu da kari kuma yawan mata masu takarar bai zarce kashi daya bisa goma na illahirin masu gwagwarmayar neman kujera a majalisar ba. Ba shakka wadannan mata in har sun samu ikon shiga majalisar dokokin zasu kawo wata sabuwar guguwa ta canjin manufofi a kasar ta Kuwait, musamman ma a bangaren yaki da cin hanci, wanda shi ne batun da aka fi mayar da hankali kansa a yakin neman zaben.