1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma na kada kuri'a a zaben Burtaniya

Salissou BoukariMay 5, 2016

A wannan Alhamis din ce al'ummar birnin London ke kada kuri'a a zaben magajin garin birnin, inda ake sa ran wani Musulmi ne zai yi nasara a zaben a karon farko.

https://p.dw.com/p/1Iikj
London Wahl des Bürgermeisters
Hoto: Reuters/S. Wermuth

Tuni dai sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a ya nunar cewa Sadiq Khan wanda Musulmi ne dan asalin kasar Pakistan, zai yi nasara a zaben da maki 10 a gaban abokin hamayyarsa dan jam'iyyar masu ra'ayin rikau kuma dan hamshakin mai arzikin nan na kasar Zac Goldsmith.

Tun dai da sanyin safiya ne 'yan takarar biyu na masu neman shugabancin birnin na London suka kada kuri'arsu, inda ake sa ran rufe rumfunan zaben da misalin karfe tara na dare agogon GMT, sannan a yi jiran sakamako zuwa yammacin ranar Jumma'a. Ana ganin idan har Sadiq Khan dan shekaru 45 da haihuwa ya ci wannan zabe, zai kasance magajin gari na farko Musulmi da zai jagoranci birnin na London.