1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisar Zimbabwe

March 31, 2005

Rahotanni sun ce komai na tafiya ba tare da tangarda ba a zaben majalisar kasar zimbabwe

https://p.dw.com/p/Bvcc

A cikin murna da farin ciki, shugaba Mugabe ya karyata korafin da ‚yan hamayyar ke yi a game da magudi a zaben kasar ta Zimbabwe. Ya ce wannan zance ne na kawai kuma yayi imanin cewar jam’iyyarsa ta ZANU-PF zata lashe kashi biyu bisa uku na dukkan kuri’un da za a kada a zaben. A lokacin da yake bayani a wata rumfar zabe dake yankin Highfield a kusa da Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, shugaba Mugabe ya ce jam’iyyarsa zata cimma gagarumar nasara, kuma kamar yadda kowa-da-kowa ke gani komai na tafiya a cikin lumana da kwanciyar hankali, ba wata rigima. Shi ma shugaban ‚yan hamayya Morgan Tsivangirai ya bayyana irin wannan karfin guiwa game da cimma nasarar zaben lokacin da ya shiga jerin daruruwan mutanen da suka jeru domin jefa kuri’unsu a rumfar kada kuri’ar da aka shirya a wata makaranta dake birnin Harare. Ya ce ko da yake ba a dora zaben akan hanyar gaskiya da adalci ba, amma a wannan karon mutane zasu bayyana ra’ayinsu na neman canji, bayan mulki na tsawon shekaru 25 da jam’iyyar ZANU-PF tayi a kasar Zimbabwe. Abin sha’awa a game da zaben dai shi ne kasancewar yakin neman zaben ya tafi ba tare da an zub da jini ba, kamar yadda aka fuskanta a shekara ta 2000 da shekara ta 2002, inda mutane sama da 100 suka halaka, da yawa daga cikinsu daga magoya bayan ‚yan hamayya. Da yawa daga masu kada kuri’ar da aka tambayi albarkacin bakinsu sun bayyana farin ciki a game da kyakkyawan yanayin da ake ciki a zaben ba tare da tashe-tashen hankula ba. Manazarta al’amuran yau da kullum sun danganta wannan kyakkyawan yanayi da matakin da Mugabe ya dauka na neman goyan baya daga jama’a, a maimakon amfani da karfin hatsi na ci gaba da abin da Amurka ta kira: mulkinsa na danniya da kama karya. Shugaban ya lashi takobin kawar da ‚yan hamayya kwata-kwata a wannan zaben, wanda ya ce ‚yan amshin shatan piraministan Birtaniya ne Tony Blair. A mayar da martani akan wannan zargi ‚yan hamayyar suka ce zaben ya shafi maganar abinci ne da guraben aikin yi ga jama’a a wannan kasa, wadda al’amuranta ke dada fuskantar koma baya tun abin da ya kama daga shekara ta 2000, lokacin da shugaba Mugabe ya dauki matakinsa na sake rabon filayen noma da kwace gonakin dubban farar fatar kasar Zimbabwe. A zaben majalisar dokokin da aka yi a shekara ta 2000 jam’iyyar MDC ta ‚yan hamayya ta lashe kujeru 57 a yayinda ZANU-PF ta tashi da kujeru 62. Amma a karkashin daftarin tsarin mulkin kasa, shugaba na da ikon nada wakilai goma kai tsaye a majalisar, lamarin da ya ba wa ZANU-PF babban rinjaye. Kimanin mutane miliyan 5 da dubdu 800 takwas suka yi rajistar shiga zaben.