1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Senegal: An fidda sakamakon karshe

Salissou Boukari
August 5, 2017

Hukumar zaben Senegal ta sanar da sakamakon karshe na zaben 'yan majalisar dokokin kasar, inda gamayyar jam'iyyun da ke mulki a kasar suka samu kujeru 125 daga cikin kujeru 165 a majalisa.

https://p.dw.com/p/2hkHj
Senegal Dakar Wahl
Zaben 'yan majalisar dokoki a SenegalHoto: picture-alliance/abaca

Gamayyar jam'iyyun da ke goyon bayan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, su kuma sun samu kujeru 19 sannan gamayyar jam'iyyu da ke goyon bayan magajin garin birnin Dakar Khalifa Sall da ke tsare a gidan kaso su kuma sun samu kujeru bakwai. Sai dai wannan sakamako da hukumar zaben kasar ta Senegal ta bayar zai samu amincewar kotun tsarin mulkin kasar ne kafin ya kasance na dindindin. Tuni bangaran Khalifa Sall ya yi watsi da wannan sakamakon. Tun dai daga ranar Litinin da ta gabata ne bangaran masu mulkin suka yi shelar lashe zaben,  inda suka ce sun yi nasara a jihohi 42 daga cikin jihohi 45 na kasar.