1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki a Jamhuriya Demokardiyar Kongo

July 30, 2006
https://p.dw.com/p/Buof

A Jamhuriya Demokradiyar Kongo, a na ci gaba da kada kuria´a zaben shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki.

Rahotani daga sassa daban-daban na ƙasar sun ruwaito cewa, zaɓen na wakana lami lafia, saɓanin yadda wasu su ka hango.

A jimilci, mutane fiye da milion 25, ya cencenta su zaɓi shugaban ƙasa, daga cikin yan takara 33, sannan su zaɓi yan majalisun dokoki 500, daga jerin yan takara kussan dubu 10.

Masharahanta a kan harakokin siyasar wannan makekiyar ƙasa, na hasashen cewa shugaban riƙwan ƙwarya mai barin gado, wato Joseph Kabila, na da sa´ar yin tazarce, ta la´akari da goyan baya, da ya samu daga al´umma.

Saida babar jama´iya adawa ta UPDS ta ƙauracewa wannan zaɓe, bayan zargin da ta yi an tabka magudi a cikin sa.

A dangane da batun tsaro, Majalisar Ɗinkin Dunia, ta tanadi sojoji fiye dubu 17, tare da taimakon rundunar tsaro ta ƙungiyar gamayya turai, da yan sanda dubu 80 na ƙasa.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Tabon Mbeki, wanda yayi ruwa, yayi tsaki a yunƙurin sassanta rikicin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ya bayana farin ciki da zaɓen.

Tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a Jamhuriya Demkoradiyar Kongo,ta bayyana girka komitin dattawa, wanda zai taimaka wajen tabbatar da shawarwarin wanzuwar kwanciyar hankali bayan zaɓen.

Komitin, da tsofan shugaban ƙasar Mozambique Joakim Chissano ke jagoranta, ya ƙunshi masu faɗa aji, a nahiyar Afrika, da su ka haɗa da tsofan shugaban ƙasar Benin Nicephore Soglo, da tsofan praministan ƙasar Senegal Mame Boye.