1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Benin

Zainab A MohammedMarch 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7c

BENIN

A yau ne ake gudanar da zaben shugaban kasa a janhuriyar Benin,karamar kasa dake yankin yammacin Afrika,domin maye gurbin shugaba Mathieu Kerekou,wanda ake bayyanawa da kasancewa tsohon mai mulkin kama karya ,wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 30 cikin shekarunta 34.

Mai shekaru 72 da haihuwa Kerekou dai ya tsufa,saboda neman zarcewa bisa ga kundin tsarin mulkin kasar na democradiyya,kuma saukarsa daga wannan mukami zai bawa alummar kasar da suka cancanci zabe million 4,damar zaban daya daga ccikin yan takara 26 dake wannan mukami.

Tun da safiyar yau nedai aka fara kada kuriu a cibiyar hada hadan kasuwancin kasar dake Cotonou,inda mutane sukayi jerin gwanno suna jiran fara kada kuriunsu,wanda ya samu jinkiri saboda rashin bayyana jamian zaben.Rahotanni daga janhuriyar Benin din dai na nuni dacewa an samu jinkirin saboda matsaloli na sufurin kayayyakin zabe.

To sai dai bayan kada kuriarsa shugaba Kerekou,ya tabbatarwa alummar kasar cewa zaa kidaya kuriu da aka kada bisa gaskiya da adalci koda zai dauki lokaci ne ana gudanar da hakan.