1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Bolivia

December 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvG0

A yau ake gudanar da zaben shugaban kasa na gaba da wa´adi a Bolivia. Kimanin masu zabe milian 3.6 ake sa ran zasu kada kuri´a a zabukan da suka hada da na shugaban kasa da na majalisun dokokin kasa da na jihohi da kuma na gwamnoni. Kuri´ar jin ra´ayin jama´a da aka gudanar ta nunar da cewa shugaban manoman ganyen koka mai ra´ayin gurguzu Evo Morales ke kan gaban sauran abokan takararsa. Shi dai Morales babban mai sukar lamirin gwamnatin Amirka ne. To amma da yake Morales ba zai samu rinjayen yawan kuri´u ba watakila majalisar dokoki ce zata zabi sabon shugaban kasar. A saboda haka masu lura da al´amuran yau da kullum ke hasashen cewa tsohon shugaban kasar Jorge Quiroga ka iya kayar da Morales, idan ya kulla kawance da kananan jam´iyu.