1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Faransa

April 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuN9

A yau alumar faransa suka fara kada kuria a zaben shugaban kasa inda ake fafatawa tsakanin yan takara hudu wadanda suka hada da Nicolas Sarkozy mai tsatsauran raáyin rikau, da Segelone Royal ta jamíyar gurguzu kuma mace ta farko dake neman wannan mukami, da Francois Bayrou mai sassauncin raáyi da kuma Jean Marie Le Pen mai matsakaicin raáyin rikau. Yan kasar Faransan miliyan 44 ne wadanda suka cancanci yin zabe suke kada kuriá a zaben na yau. Tuni aka fara kada kuriár a wasu kasashen ketare inda faransawa kimanin 900,000 suka fita domin jefa kuriár su. Idan kamar yadda aka yi tsammani babu wani daga cikin yan takarar da ya sami gagarumin rinjaye a zaben to zaá sake karawa a ranar 6 ga watan Mayu a tsakanin manyan yan takara biyu wadanda ke kan gaba. Batutuwa na dumbin bashi dake kan gwamnati da rashin aiki da kuma rashin ingantattun walwalar jamaá da batun yan gudun hijira na daga cikin alámuran da suka dabaibaye gwagwarmaya a fafutukar yakin neman zabe domin samun wanda zai gaji shugaban kasar mai barin gado Jacques Chirac.