1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Haiti

February 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv90

A kasar Haiti, a na ci gaba da zaben shugaban kasa na farko, tun bayan hambarar da shugaba Jean Bertrin Aristide a shekara ta 2004.

Majalisar dinkin dunia ta kasashe masu hannu da shuni, mussamman Fransa, da ta yi wa Haiti mulkin mallaka na burin ganin zaben ya gudana lami lahia.

Karro 4 daban daban, a na dage shi, a tsawon shekara da ta gabata, dalili da rashin issasun mattakan tsaro.

Kiddidigar bayan fage da ka gudanar na nuni da cewa tsofan shugabankasa Rene Preval ztai nlashe wanna zabe, ta la´akari da yada ya ke da dimin masu goyan baya.

Wannan zaben na gudana, a yayin da hambararen shugaban kasa, Jean Bertri Aristide ke zaman gudun hijira a kasar Afrika ta kudu.

A karfe 9 na dare agogon GMT, a ke ruhe rufunan zaben.

Kuma a na sa ran samu sakamokon karshe, nan da kwanaki 3 masu zuwa.

Majalisar dinkin dunia ta kai dakarun kwantar da tarzoma, domin ganin mutane ,kimanin million 3 da rabi, da ya cencenta su ka kuri´u, sun yi hakan cikin kwanciyar hankali.