1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Haiti

November 28, 2010

'Yan takara 19 za su fafata a zaben shugaban kasa zagaye na farko a Haiti.

https://p.dw.com/p/QKFU
Rene Preval Futacen shugaban kasar Haiti mai barin gadoHoto: AP

A  kasar Haiti  a yau ake gudanar da zaben shugaban kasa wanda akansa yan takara 19 zasu kara a zagaye na farko domin maye gurbin Shugaba Rene Preval wanda ya kammala wa'adin mulkinsa. Masu aiko da rahotannin sun ce daga cikin yan takara da ake da su babu wani wanda ake tsamanin zai samu gagarumin rinjaye  tun a zagayen farko a la dole sai an kai ga yin zagaye na biyu.

Ana gudanar da wannan zabe ne dai bayan girgizar kasa da ta kashe mutane 1 230 sanan kuma ga cutar amai da gudawa ta kwalara da ta hallaka sama da mutane dubu daya kawo yanzu.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita        : Abdullahi Tanko Bala