1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Jamus 

Ahmed Salisu
February 11, 2017

A Lahadin nan ce ake zaben shugaban Jamus domin maye gurbin shugaba mai ci Joachim Gauk wanda wa'adin mulkinsa ya zo karshe. Shin wacce irin rawa shugaban kasa ke takawa a Jamus? Meye banbancinsa da shugaban gwamnati?

https://p.dw.com/p/2XPGU
Deutschland Bonn Bundesadler
Hoto: DW/L. Sanders

Mukamin shugaban kasa a tarayyar Jamus dai matsayi ne da ke da kima sai dai a tsarin gudanar da mulki na kasar ba shi ba ne wanda ke kan gaba ba wajen karfin fada a ji a kasar sabanin yadda ake da shi a lokutan baya. Mafi akasari shugaban kasa a Jamus kan kasance ya nesanta kansa daga harkoki na siyasa wanda hakan ya sanya a ke kallon ofishinsa a matsayin wata alama ta hadin kan kasa. Duk da cewar shugaban kasa kan wakilci kasar a kasashen ketare a wasu sabgogi da suka shafi Jamus kana ya kan maida hankali wajen cigaban demokradiyar kasar da kuma tabbatar da mutunta dokokin da aka shimfida a kasar, bisa ga yadda dokokin kasar suke wanda ke rike da mukamin shugaban gwamnati ne ke tafiyar da lamura na yau da kullum na sha'anin mulki a Jamus.

Deutschland Abschiedsrede von Bundespräsident Gauck
Shugaban tarayyar Jamus mai barin gado Joachim GauckHoto: Reuters/H. Hanschke

Duk da cewar shugaban kasa a Jamus ba ya tafiyar da harkokin mulki na yau da kullum, ya kan kasance wanda ke sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi na kasa da kasa da suka shafi Jamus kuma shi ne ke sanya hannu kan wasu dokoki da majalisar dokokin kasar suka amince da su. Har wa yau shugaban kasa a Jamus kan tsoma baki kan wasu abubuwa da ke damun kasar da ma na wasu kasashen ketare ciki kuwa har da batun wanzar da zaman lafiya da hadin kan kasar da sauran kasashe da kuma batu da ya dangaci kare muhalli.

Frank-Walter Steinmeier besucht bayerischen Landtag
Frank-Walter Steinmeier na zawarcin kujerar shugaban kasar JamusHoto: picture-alliance/dpa/S. Hoppe

Idan ya kasance an shiga rudani na siyasa a Jamus shugaban kasa shi ne ke da alhaki na gudanar da zabe musamman ma idan wanda ke rike da mukamin shugabar gwamnati ya rasa tudun dafawa a majalisar dokoki wato ya rasa rinjayen da ya kamata a ce ya na da shi, sai dai shugaban kasa a Jamus ba shi da karfin iko na saukewa ko nada ministoci ko alkalai ko kuma wasu manyan jami'an gwamnati. Bisa ga wannan dai ma iya cewa shi shugaban Jamus uba ne na kasa wanda da dama kan ta'allaka gare shi wajen ganin kasar ta kasance tsintsiya madaurinki daya. 

A zaben na yau dai ba mutum guda ne ke neman wannan matsayi ba amma kuma alamu na nuna cewar Frank-Walter Steinmeier ka iya kasancewa sabon shugaban Jamus duba da irin ficen da ya yi da kuma karfin fada da yake da shi.