1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Liberia gobe talata

Zainab A MohammadOctober 10, 2005

Zabe a karon farko bayan cimma sulhu

https://p.dw.com/p/BvZ0
Hoto: AP

A halin yanzu dai ana iya cewa aski yazo gaban goshi a dangane da shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a Liberia,wanda zai gudana gobe talata.

A gobe talata nedai alummar kasar Liberia,zasu kada kuriunsu domin zaban wanda zai jagorancesu tsakanin tsohon jarumin wasan kwallon kafa ,kuma tsohon jamiin babkin duniya da kuma mai jagorantare shugabannin hauloli da yan kasuwa.Dukkannin yan takaran biyu dai sunyi alkawarin sake ginin kasar ta Liberia da yaki ya ragargaza,tare da tsamota daga kangin talauci.

A jiya lahadi nedai aka kawo karshen kamfaign na yakin neman zabe a hukumance,da akasarin yan takara 22 a churchi domin neman goyon bayan yan kasar million 1. Da dubu dari da sukayi rigista domin kada kuriun nasu a wannan kasa dake yammacin Afrika mai yawan alumma Million uku.

Ana dai kyautata zaton cewa zaben na shugaban kasa dana yan majalisar dokoki ,bisa da yarjejeniyar sulhu da aka rattaba hannu tsakanin bangarori 3 dake yakan juna a watan Augustan 2003,nada nufin mayar da rikicin kasar da mulkin danniya data fuskanta a baya cikin littafinta na tarihi.Wadannan rikice rikice dai sun zubar da jinin dubban alummar wannan kasa ,banda dumbin miliyoyin dalolin a matsayin kudaden shiga da akayi asarar su.

An dai gudanar da harkokin yakin neman zabe cikin lumana,da kasancewa dakarun kiyaye zaman lafiya dubu 15 na mdd tun daga watan oktoban 2003,domin tabbatar da ingantaccen tsaroi,batu kuma daya bayyana cewa hanyar ta doshi zaman lafiya.

Rahotanni dai na nuni dacewa fitattccen dan takara wanda kuma ake hasashen ganin cewa shine zaiyi nasara saboda kwarewarsa a kwallon kafa da kuma martaba dayake dashi a idon jamaa na kishin kasa ,George Weah,shine keda mafi yawan goyon baya,sai kuma yan takara da suka hadar da Roland Massaquoi,daga jammiyar tshon shugaban kliberia Charles Taylor.

Yan takaran dai na musayan hanya acikin birane,ayakin neman zaben nasu na karshe a jiya ba tare da wani tashin hankali ba.

George Weah dai nada goyon bayan matasa,wadanda suke zama kashi 2 daga cikin 3 yawan wadanda suka cancanci zaben,wadanda kuma sukayi watsi da batun cewa bashi da ilimin zamani,kuma bashi da masasniya dangane da harkokin siyasa,inda suke cigaba da bayyana alfaharinsu dangane da irin hidimomi dayakewa kasar tasa,da kuma goyon baya musamman lokutan yaki.

A ranar asabar dai sama da matasa dubu 100 sukayi jerin gwanon yimasa kamfaign cikin ruwan sama da guguwa,sanye da riguna dake dauke da hoton fuskarsa.

Kasar ta Liberia dai na cikin halin kaicho sakamakon rashin wutan lantarki,da kayayyakin more rayuwa da rashin ruwabn sha mai tsabta da rashin makarantun koyarwa,banda kuma batun asibitoci a hannu guda.

Bayan gudanar da zaben gobe talata dai,anasaran samun sakamakon karshe ranar 25 ga wannan wata,idan har baa samu dan takara daya samu nasara da mafi yawan kuriu wandfa yawansu yakai kashi 50 daga cikin 100 na wadanda aka kada ba,zaa sake zaben fitar da gwani aranar 8 ga watan Nuwamba.

To sai dai manazarta na ganin cewa koda wane irin sakamako wannan zabe zai haifar tsugune bata karewa Liberian ba,domin ainihin aikin na gaba,domin wannan shine mafari kawai.