1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a masar

zainab A MohammadSeptember 7, 2005

Shugaba Hosni Mubarak yayi takara a karo na biyar

https://p.dw.com/p/BvZs
Hoto: AP

A yau ne alummar kasar masar suka kada kuriunsu ,a karo na farko domin zaben shugaban kasa.Zaben da akayi hasashen cewa shugaba Hosni Mubarak dake zama daya daga cikin yan takaran zai lashe.

Hukumar zaben masar din dai ta yabawa yadda alummar kasar suka fito domin tabbatar da yancinsu nay an kasa ta hanyar zaben shugaba daya fi dacewa way a jagorancesu.To sai dai akwai rahotannin rudadi ,domin masu kada kuriu sunyi ta yawo suna neman cibiyoyin zabe,ayayinda wasu masu lura suka sha duka,kana wasu kuma suka fuskanci bincike.

Shugaba Hosni Mubarak mai shekaru 77 da haihuwa kuma tsohon commandan rundunar dakarun sama ,wanda ya shugabanci kasar cikin shekaru 24 da suka gabata ,ya kasance mutumin farko daga cikin yan takara 10 ,daya kada kuriarsa a yau.

Babban abokin adawa dake kalubalantarsa ,a wannan matsayi dayake nema a karo na biyar,daga jamiiyar Ghad Ayman Nur mai shekaru 40 da haihuwa ,ya bayyana wannan zabe da kasancewa babban batu a tarihin masar.

Wannan shine karo na farko da shugaba Mubarak ya fuskanci kalubale ,tare da matsin lambar cikin gida da ketare ,a dangane da gyare gyare cikin harkokin mulki,a kasar da har yanzu ake gudanar da mulki irin na kama karya tun bayan kisan gilla da akayiwa tsohon shugaba Anwar Sadat a shekarata 1981.

Wadanda suka lura da yadda harkokin zaben ya gudana a birnin cairo dai basu ce komai ba a dangane da sakamako,amma jamiai sunce sakamako bazai samu ba har zuwa gobe,wata kila da dare.

Duk dacewa babu adadin mutane da suka fito domin kada kuriunsu,daga cikin kimanin million 32 da suka cancanci zabe,manema labaru da kungiyoyi masu zaman kansu na masar da suka ganewa idanunsu yadda lamarin ya gudana,sunyi bayanin cewa mutane kalilan ne suka bayyana a cibiyoyin zaben dake birane da manyan garuruwa ,idan aka kwatanta da yadda mazauna kauyuka sukayi dafifi a nasu cibiyoyin zaben.

Komitin gani da ido mai zaman kanta ta sanar dacewa an baje kayayyakin campaign a wajen cibiyoyin zabe kashi 90 daga cikin 100,sabanin dokar gudanar da zaben.

Ayayinda shi kuwa babban jamii dake jammiyyar Mubarak Ahmed Azz,ya bayyana cewa jammiiyar mulkin kasar na gudanar da campagn cikin kasar baki daya,domin tabbatar dacewa magoya bayanta million 12 sun kada kuriunsu a zaben na yau.

Akwai koke koke daga jammiiyun adawa dangane dacewa ,wasu sun isa cibiyoyinsu domin kada kuriunsu,amma sukan tarad da cewa tuni akayi amfani da sunansu wajen kada kuriu.Wasu alummar kasar da sukayi hira da manema labaru sun bayyana muradinsu na samun sabon shugaba,bayan shekaru 24 ana mulki irin na danniya.

Yanzu dai an sanya idanu domin ganin yadda zata kaya a dangane da sakamakon wannan zabe na shugaban kasa a Masar,wanda jamiai sukace zai kai gobe alhamis da dare.