1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Rasha

Umaru AliyuMarch 3, 2008

Sakamakon zaben Rasha bai bada mamaki ba

https://p.dw.com/p/DHYF
Sabon shugaban Rasha, Dmitri MedvedevHoto: AP

Dan takarar da fadar mulkin Kremlin a Rasha ta tsayar, Dmitri Medvedev shine ya sami nasarar lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar Lahadi. Tun kafin zaben aka tabbatar da cewar Medvedv, dan shekaru arba'in da biyu shine zai sami nasara, bayan da Vladimir Putin, shuigaban Rasha mai barin gado, ya baiyana cikakken goyon bayan sa gareshi. To sai dai jam'iyun adawa sun kwatanta zaben da aka yi a matsayin mummunan cuta. Wadanda suka lura da yadda zaben ya gudana, suka ce an sami magudi mai yawa a lokacin kada kuri'un. Umaru Aliyu ya fassara sharhin da Cornelia Rabitz ta rubuta..


Sakamakon zaben dai bai baiwa kowa mamaki ba. Bugu da kari kuma, tun ma kafin zaben aka san yadda sakamakon sa zai kasance. Sabon shugaban Rasha dai shine Dmitri Medvedev. Nan gaba kadan kuma ba zamu yi mamaki ba, idan aka nada Vladimir Putin a matsayin sabon Pirayim minista.
Sai dai duka wadannanal'amura ne da babu wani abin fda ya dangantaka su da democradiya, muddin tsarin demokradiyar yana aiki, saboda babu wani abin zabi na hakika a kasar ta Rasha. Al'ummar Rasha an nemi su tabbatar da wanda aka zaba ne domin ya gaji Putin: sun kuwa aiwatar da wnanan nauyi da aka dora kansu, tare da sanin cewar babu wani abin da zai canza a mulkin na Rasha, wato komai zai ci gaghba da zama jiya i yau.
Putin, kamar yadda mutane da yawa suka yi imani, ya kawowa Rasha jin dadin rayuwa da kwanciyar hankali. Magajin sa Medvedev, shima suna fata zai ci gaba a haka, daga inda Putin ya mika masa. A fadar mulki ta Kremlin, shugabannin suna iya fitowa su bugi kirjinnunawa duiya cewarf sun bi dokoki da tsarin mulkin Rasha sau da kafa a wannan canji da suka aiwatar.
Yanzu dai idanun duniya gaba daya zai tattara ne kan Dmitri Medvedev ta5rte da tambayar: shin ina zai fi maida alkiblar aiyukan sa, wadanne abubuwa zai fi baiwa fifiko. Shin, kamar yadda tun yanzu aka ta nuna alamun cewar zai karkata zuwa ga kasashen yamma, zai yi hakan, ya kasance mai matsakaicin ra'ayi. Shin ko nan gaba kadan zai kasance mai cin gashin kansa daga shisshigin Vladimir Putin, mutumin da ya dora shi kan wannan mukami.
Ana dai shakkar haka, saboda ya zuwa yanzu, babu wasu alamu da suka nuna cewar Medvedev zai iya karbar madafun ikon kasar ta Rasha gaba daya a hannun sa. Ko a lokacin kampe na zaben, Medvedev, wanda Putin ne ya rene shi a fannin siyasa, ya kasa nuna wata alkibla ko manufa ta kashin sa. Sabon shugaban dai ana iya cewar ya kasance dan wata zuriyar ce dabam da wanda zai gaji mukamin a hannun sa, saboda shi din bashi da kwarewa a hukumar leken asiri ta kasar.
Medvedev zai kasance a shugabancin kasar da Putin tsawon shekaru takwas ya jagoranci aiyukan ta na zaman ta da manufofin ta da kura-kuran ta. A tsakanin wadannan shekaru an raunana manufofi na democradiya da tsarin tsari'a an tauye aiyukan kungiyoyi masu zaman kansu, yayin da yan leken asiri suka kutsa al'amura na siyasa da tattalin arzikin kasar. Bunkasar tattalin arzkin da ake yabawa Putin da kawowa kasar ta Rasha, ta dogara ne kan cinikin man fetur da gas, wanda ko a wannan fanni ma, wasu yan kasar kalilan suka kara azurta, mafi yawan Rashawa kuma suka kara shiga hali na tsananin talauci. Saboda haka, sabon shugaban yana da gagatrumin aki a gaban sa. abin dake iya zama wata dama a gareshi ta tabbatar da daidaituwa a wannan kasa, tare da samun damar kyautata dangantaka da Amerika a manufofin sa na harkokin waje. Bisa manufa dai Medvedev zai yi aikin sa ne bisa hadin gwiwa da Pirayim minista Vladimir Putin. Sai dai abin tambaya shine: shin Putin din zai yarda da gaskiyar cewar daga yanzu, Medvedev shine yafi karfin iko a harkokin siyasar kasar ta Rasha. Duk kuwa wanda a lokacin kampe na neman kuri'u ya lura da yadda Putin da Medvedev suka rika nunawa jama'a yadda zasu hada gwiwar tafiyar da manufofin su, zai yi shakkar ko Putin din zai mika harkokin mulki gaba daya ga sabon shugaban, wanda ma shine ya dora shi kan wannan mukami.