1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Ruwanda

Simone Schlindwein SB
August 4, 2017

An gudanar da zaben shugaban kasa a Ruwanda lamarin da zai tabbatar da Shugaba Paul Kagame wanda ya shafe shekaru 14 kan madafun iko.

https://p.dw.com/p/2hiN7
Ruanda Wahlkampf | Paul Kagame Anhänger
Hoto: DW/S. Schlindwein

'Yan kasar Ruwanda na zaben shugaban kasa, kuma tuni ake hasashen Shugaba Paul Kagame wanda ya shafe shekaru 14 kan madafun iko zai kuma lashe zaben. Sai dai a wannan karo dan takara na jam'iyyar masu kare muhalli yana neman gwada sa'a a zaben ganin yadda ya ke fafatawa da shugaba mai ci. Jagoran jam'iyyar adawar Frank Habineza dan shekaru 40 shi ne ke kokarin ganin ya kayar da shugaba mai ci Paul Kagame a wannan zaben da ake gani zai yi wuya wannan dan adawar ya ma kai labari, saboda yadda farin jinin Kagame ke karuwa da kuma yadda ya lashe zaben da ya gabata da gagarumin rinjaye. zaben shugaban kasa a Ruwandan na daya daga cikin muhimman lamuran siyasar Afirka da duniya ta mayar da hankali a kai a wannan shekarar, ganin cewar ba wai Ruwandan ta kasance daya daga cikin kasashen da suka yi saurin farfadowa bayan yakin basasa.

Jagoran adawa ya yi ikirarin samun nasara

Ruanda Präsidentschaftswahlen Frank Habineza
Jagoran adawa Frank HabinezaHoto: Reuters/C. Uwiringiyimana

Tun bayan kisan kare dangi na shekara ta 1994, jam'iyyar RPF ta karbi ragamar jan akalan kasar. Jam'iyyar da ta samu tushe daga tsoffin sojojin tawaye, wadanda suka cimma nasarar kawo karshen kisan gilla da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi marasa rinjaye, kuma a yau shugabanta Paul Kagame shi ne mutum mafi karfi a Ruwanda, wanda ke shugabanci tun daga shekara ta 2000, bayan rike kujerar mataimakin shugaban kasa da kuma ministan tsaro.Wannan jam'iyya ta kare muhalli tana cikin jam'iyyun adawa biyu da aka amince da su a Ruwanda. Shi dai dan adawa Frank Habineza ya koma gida Ruwanda a shekara ta 2013 bayan gudun hijira da ya yi a kasar Sweden inda ya samu nasarar yi wa jam'iyyarsa rijista, duk da cewa babu alama na cewa jam'iyyar ta masu kare muhalli za ta iya samun nasara, sai dai yunkurinsu na shiga zaben kansa abune da masana ke ganin nasara ce ga bangaren adawa a kasar da ake dakile duk wata dama daga bangaren 'yan adawan. Masana dai na ganin 'yan adawa sun nuna sabon salo na zabe ga 'yan Ruwanda maimakon salo na kama karya da aka dadde ana zargin Shugaba Paul Kagame da yi, Jagoran jam'iyyar adawa Frank Habineza ya ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare saboda haka ba zai fidda zato na lashe zaben shugabancin kasar ta Ruwanda ba.